Taskar rubutukan malamai

Yanda za’a kama Manara Tv da Manara Radio.

Assalaamu Alaikum warahmatullah wabarakaatuh ‘yan’uwa Albishirinku. Ga wata Sabuwa! Kungiyar Izala ta bude sabuwar Tashar Radio da talabijin. Manara TV kafa ce ta talabijin dake kan tauraron dan Ad…

Source: Yanda za’a kama Manara Tv da Manara Radio.

Advertisements
Standard
Fadakarwa/Tunatarwa, Taskar rubutukan malamai

FADAKARWA GA ‘YAU UWA MUSULMI

1). Karka rinka yin fitsari a wurin
da kake yin wanka, domin hakan
yana gadar da yawan mantuwa.
(2). Karka rika kwantawa barci
bayan ka cika cikinka da abinci,
domin yin hakan yana gadar da
mutuwar zuciya. (3). karka rika
yawaita kallan al’auranka ko ta
wasu, domin yin hakan yana sa
dakikanci da nauyin kwakwalwa
wajen fahimtar abubuwa. (4.).
kar karika yin bacci bayan sallar
asuba har sai rana tafito, domin
yin hakan na janyo tsiya da
talauci. (5). kar ka sha madara
bayan kaci kifi, domin yin hakan
yana gadar da kuturta. (6). karka
ci ko sha alhali kana da janaba,
domin yin hakan makarohi ne,
kuma yana jawo raunin jiki. (7)
karka rika hassada ko
munafunci da ha’inci, domin
suna da hatsari ga lafiya, sukan
kuma haifar da cutar hauka,
gashi kuma suna bata ayyuka
masu kyau. (8). karka rika yawan
kukan babu ko ka yi ta tallan
talaucinka afili. Yin hakan yakan
dawwamar da mutum cikinsa.
(9) karka rika kwanciya barci
alhali kana jin fitsari, yin hakan
yana haifar da mutuwar
mazakuta. 10. kayi amfani dasu
domin zasu

Standard
Fadakarwa/Tunatarwa, Taskar rubutukan malamai

ALLAH KA AZURTAMU DA HALAL, KUMA KA KAREMU DAGA CIN HARAMUN,… (Sheikh Isa Ali Pantami)

ALLAH KA AZURTAMU DA HALAL,
KUMA KA KAREMU DAGA CIN
HARAMUN,…
Annabi (SAW) yana cewa: Kowace
AL’UMMAH tana da FITINA a
cikinta. Amma FITINAR wannan
AL’UMMAH, itace KUDI. (Abu-daud
RH da Tirmithiy RH sun ruwaito
shi, kuma Shaykh Albaniy RH ya
inganta hadith din).
Yaa Allah ka azurta damu da
HALAL, ka karemu daga cin
HARAMUN,…

Standard
Fadakarwa/Tunatarwa, Taskar rubutukan malamai

SADAKA A LOKACIN JINYAN MARAR LAFIYA SUNNAH NE: Yaa Allah ka bamu karin lafiya da Imani,… (Sheikh Isa Ali Pantami)

SADAKA A LOKACIN JINYAN MARAR
LAFIYA SUNNAH NE: Yaa Allah ka
bamu karin lafiya da Imani,…
Annabi (SAW) yana cewa: Kuyi
jinyar MARASSA LAFIYANKU da
bada sadaka.
(Abu-Daud ya ruwaito, Shaykh
Albani ya inganta shi a Sahihul-
Jamiy 3358).
Yana daga karantarwar Sunnah,
Idan muna jinyar iyaye ko Iyalai
ko yan’uwa, mu yawaita bada
Sadaqa, Domin Allah yana bada
lafiya ta wannan hanyar. Yaa
Allah ka amsa mana addu’o’in
mu da bukatunmu,…

Standard
Fadakarwa/Tunatarwa, Taskar rubutukan malamai

Alamomin tashin Al- kiyamah guda ‘Dari 100 kashi na biyu (2) (Mal.Aminu Ibrahim Daurawa)

51.
Wani Zamani da mutum zai kwana Mumini
ya wuni kafiri;- saboda mafi yawan
maganganu da aiyuka da ba sa kan
Shari’ah 52. ‘Kawata Masallatai da yin gasar
Hakan (kaji ana Masallacin mu yafi naku
kyau) 53. ‘Kawata gidaje da yi musu
kwalliya 54. Yawan Saukar Kwarankwatsa
da Aradu 55. Yawan Rubuce-Rubuce;-
Ya’duwar Rubutuce-Rubuce marasa amfani
(jaridu da mujallu, da littafai da internet) ba
a tunanin amfanin rubutun kawai da an
rubuta 56. Wanda suka ‘kware a ro’ko da
ziga, su suka fi samun ku’di 57. Za shagala
da karanta wasu abubuwa a bar Al’qur’ani
58. ‘Karancin Malaman fi’khu da yawan
Gardawa 59. Neman Ilimi a wajen ‘kananan
mutane;- ‘karamin Mutum wanda ba ya aiki
da ilimin sa 60. Yawan mutuwar ba-zata 61.
Shugabancin Wawaye (kuma suna ganin
kan su wayaiyu) 62. Lokaci zai dinga sauri
63. Banzaye za su mamaye kafafan ya’da
labarai;- Mutumin da ba kowa ba, kuma bai
zan komai ba, zai dinga magana kan
abubuwan da suka shafi Al’ummah 64.
Ma’daukaki a duniya shine banza ‘dan
banza;- kaga ana ta rububin wani wanda
bai da amfanin komai saboda wani shirme
da yake Misali;- ‘Yan Bal da Mawa’ka 65. Mai
da cikin masallatai Hanyoyi 66. Sadakin Aure
zai yi tsada, sai kuma ya zo yai arha 67.
Dawakai za su yi tsada sai kuma su zo su yi
arha 68. Kasuwanci zai yi sau’ki (ta yadda
zaka sai Abu ko ka sayar daga ‘dakin ka, ba
tare da ka je ko ina ba) Misali;- yanar gizo
69. Kafiran duniya za su yi taron dangi akan
musulmi 70. Mutane za su dinga gudun
limanci a cikin Sallah (saboda ba cikakken
Albashi) 71. Aukuwar Mafarkin Mumini (in
Mumini yai mafarki sai Abu ya faru 72.
Yawan ‘karaya 73. yawan gaba 74. Girgizar
‘kasa 75. Yawan Mata 76. ‘Karancin Maza
77. Aikata Sa’bo a filigahh 78. Mai da
karatun Al’qur’ani hanyar Neman ku’di 79.
‘Kiba, mutane za su yi ta ‘kiba mai yawa 80.
Bayyanar mutane masu yin shaida tun ba a
tambaye su ba 81. Masu Bakance ba sa
cikawa 82. Masu ‘karfi za su danne raunana
83.’Rashin Hukunci da Alqur’ani 84. Yawan
rumawa da ‘karancin larabawa 85.
Ya’duwar ku’di 86. ‘Kasa za ta fitar da
taskokin ta 87. MòZa a dinga shafe halittar
wasu mutane suna komawa wata 88.Halitta
daban 89. Tsagewar ‘kasa, ta ha’diye
mutane 90. Wasu ‘kwarangwazai,
duwatsun da ba a San su ba za su dinga 91.
fa’dowa mutane aka 92. Yawan ambaliyar
ruwa 93. Ruwan ‘bala’i;- wanda ba ya fidda
shuka ko tsiWwFitina da za ta 93.wata
fitina za ta’barke tsakanin larabawa Har ta
kusa ‘karar da su 94. Bishiya za ta yi
magana don taimakawa musulmi 95. Dutse
zai magana don taimakawa musulmi 96.
Ya’kin Musulmi da Yahudu 97. Kogin furat
zai ‘kafe, a hango Dutsen Gwal a ciki 98.
Zamanin da za a yiwa masu addini kallon ba
wayayyu ba 99. ‘Kasashen larabawa za su
samu ci-gaba mai yawa 100.Bayyanar wata
Babbar fitina da zata shafi kowa Mu ha’du a
darasi na gaba Allah ya kare mu sharrin
fitintunu

Standard
Fadakarwa/Tunatarwa, Taskar rubutukan malamai

TAMBAYOYIN JARRABAWAN DA DOLE SAI MUN AMSA(Sheikh Isa Ali Pantami)

Annabi (SAW) Yace Idan mutum
ya mutu, Mala’iku biyu zasu zo
masa sannan su masa tambayoyi
Hudu a ‘Kabarinsa. Wadannan
tambayoyi sune:
1) Waye Mahaliccinka? Amsa:
ALLAH.
2) Menene addininka? Amsa:
Addini na shine Musulunci
3) Me zaka ce akan wannan
da aka aiko muku? Amsa:
Muhammad, Manzon Allah
4) Menene ilminka? Amsa: Na
karanta littafin Allah, kuma nayi
Imani da shi. Annabi (SAW) Yace
duk wanda ya amsa ko ta amsa
tambayoyin nan dai dai a ‘Kabari,
za a rubuta sunansa/ta a cikin
“ILLIYUN” wanda shine register
ta sunayen ‘yan Aljannah. (Abu
Daud, 4753; Ahmad, 18063;
Saheehul’Jamiy, 1676) Yaa Allah
ka bamu ikon amsawa dai dai
da SHIGA wannan register Mai
daraja

Standard
Fadakarwa/Tunatarwa, Taskar rubutukan malamai

ALAMOMIN KYAKYKYAWAN K’ARSHE! – sheikh isah ali pantami

Sheikh Isa Ali
Pantami
ALAMOMIN
KYAKYKYAWAN
K’ARSHE! Allah ya sa mu
cika da IMANI,..
Annabi (SAW) yana
cewa: Idan Allah yana
nufin BAWANSA da
ALHERI, sai yayi aiki da
shi. Sai aka tamabayi
Annabi (SAW) ta yaya
Allah zai yi aiki da shi?
Sai yace:Allah zai shiryar
da shi zuwa ga ayyuka
na kwarai gabannin
rasuwarsa (Imam
Ahmad, 11625; al-
Tirmidhi, 2142; saheeh
by Al-Albaani ya inganta
shi Saheehah, 1334).
ALAMOMIN CIKAWA DA
MUTUWAR SHAAHADA:
Akwai wasu alamomi
duk wanda ya rasu ya
samu dacewa da daya
daga cikinsu akwai
alamar ya samu
mutuwa mai nagarta,
kuma akwai alamun
yayi mutuwar
SHAHAADA.
1) RASUWA DA KALMAR
SHAHADA: Annabi
(SAW) yana cewa: Duk
wanda kalmar
karshensa ya zama
LA’ILA ILLA LAAH, zai
shiga ALJANNAH (Abu
Dawood, 3116; Saheeh
Abi Dawood, 2673).
2) RASUWA TA
HANYAR
MATSANANCIYAR
JINYA: Annabi (SAW)
yana cewa: MUMINI
yana rasuwa da JIBIN
GOSHI. (Ahmad, 22513;
Tirmidhi, 980; Nasaa’i,
1828).
3) RASUWA DALILIN
NAK’UDA ko RASUWA
DALILIN KOWACE CUTA
ALHALI MACE NA DA
JUNA: Annabi (SAW)
yace MATAR da ta rasu
tana da juna to tayi
SHAHADA. Duba (Abu
Dawood 3111).
4)RASUWA DALILIN
CUTAR ANNOBA: Duba
(Bukhaari, 2830; Muslim,
1916).
5) RASUWA RANAR
JUMU’AH KO DARENTA:
Duba hadisin Ahmad,
6546; al-Tirmidhi, 1074.
al-Albaani.
6) RASUWA A
TAFARKIN ALLAH: Duba
Al-Qur’an Suratu
Al-‘Imraan 3:169.
7) RASUWA DALILIN
CIWON CIKI: Duba
Sahihu Muslim, 1915.
8)RASUWA DALILIN
RUSHEWAR GINI KO
KUMA A RUWA: Duba
littafin Bukhaari, 2829;
Muslim, 1915.
9) RASUWA DALILIN
WUTA. Duba cikin
littafin Saheeh al-
Targheeb wa’l-
Tarheeb, 1396.
10)RASUWA DALILIN
KARE ADDINI KO
DUKIYA KO RAI: Duba
littafin Tirmidhi, 1421.
11) RASUWA A CIKIN
KYAKYKYAWAN AIKI:
Duba littafin Imam
Ahmad, 22813.
Yaa Allah ka mana
baiwa da kyakykyawan
karshe, sannan ka sa
mu yi MUTUWAR
SHAHADAH,…
By
Isa Ali Ibrahim Pantami

Standard