Dr. Ibrahim Jalo Jalingo, SUNNAH

MUSABAKAR HADDAR
ALQUR’ANI KO HADITHI KO
WANI NAU’IN ILMI A
MAHANGAR MUSULUNCI:
Da yawa daga cikin
wadanda suka zaba wa
kansu sabanin shiriyar
Manzon Allah cikin
gudanar da addininsu
suna ganin cewa: In har
Idin Maulidi bidi’ah ne, to
kuwa lalle Musabaka a kan
haddar Alqur’ani Mai
girma, ko haddar Hadithan
Annabi masu daraja ko
haddar wani ilmi na
Musulunci su ma yin su
bidi’ah ce!!!
***************
**********
A nan muna ganin cewa
yawan nisantar wadannan
mutane ga littattafan
Shari’ah na maluman
Musulunci ne ya sa ba su
ma san cewa: Dukkan abin
da halaccinsa ya tabbata
ta yanyar Ijma’in Musulmi
cikin wani zamani daga
cikin zamuna, to dole ne
ya zamanto daya daga
cikin abubuwa uku:-
1- ko dai ya zamanto
Mubaahi, watau abin da
yin sa da rashin yin sa duk
daya a idanun Shari’ah.
2- ko kuwa ya zamanto
Mustahabbi, watau abin
da in har ba a yi shi ba to
ba a yi wani laifi ba, in
kuma aka yi shi to ana da
wani lada na musamman.
3- ko kuwa ya zamanto
Waajibi, watau abin da in
har ba a yi shi ba za a sami
zunubi, in kuma an yi shi
to an yi abin da Shari’ah ta
tilasta yin shi.
***************
***************
shi kuwa Musabaka domin
haddar Alqur’ani Mai
girma abu ne da Maluman
Sunnah, da su kansu masu
bidi’ah na Duniya suka
hadu a kan halaccinsa a
bisa hujjar kiyasin shi a
kan Musaabakokin da
Nassi ya zo da halaccinsu.
In kuwa haka lamarin
yake, to ta kaka ne za a
hada hukuncin Musaabaka
domin haddar Alqur’ani da
hukuncin Idin Maulidin da
babu mai yin shi ko
halatta shi in banda wasu
daga cikin masu yin
bidi’ah??
*********************
HUKUNCIN MUSABAKA:
1. Imam Ibnu Qudaamah
mai rasuwa a shekara ta
620 watau da mutuwarsa
yau shekaru 815 ke nan,
ya ce cikin littafinsa mai
suna Almugnii
13/404-405 :-
{ ﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ ﺟﺎﺋﺰﺓ ﺑﺎﻟﺴﻨﺔ
ﻭﺍﻻﺟﻤﺎﻉ، ﺍﻣﺎ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﻓﺮﻭﻯ ﺍﺑﻦ
ﻋﻤﺮ ﺍﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ
ﻭﺳﻠﻢ ﺳﺎﺑﻖ ﺑﻴﻦ ﺍﻟﺨﻴﻞ
ﺍﻟﻤﻀﻤﺮﺓ ﻣﻦ ﺍﻟﺤﻔﻴﺎﺀ ﺍﻟﻰ ﺛﻨﻴﺔ
ﺍﻟﻮﺩﺍﻉ، ﻭﺑﻴﻦ ﺍﻟﺘﻲ ﻟﻢ ﺗﻀﻤﺮ ﻣﻦ
ﺛﻨﻴﺔ ﺍﻟﻮﺩﺍﻉ ﺍﻟﻰ ﻣﺴﺠﺪ ﺑﻨﻲ
ﺯﺭﻳﻖ. ﻣﺘﻔﻖ ﻋﻠﻴﻪ… ﻭﺍﺟﻤﻊ
ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻮﻥ ﻋﻠﻰ ﺟﻮﺍﺯ ﺍﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ
ﻓﻲ ﺍﻟﺠﻤﻠﺔ. ﻭﺍﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ ﻋﻠﻰ
ﺿﺮﺑﻴﻦ: ﻣﺴﺎﺑﻘﺔ ﺑﻐﻴﺮ ﻋﻮﺽ،
ﻭﻣﺴﺎﺑﻘﺔ ﺑﻌﻮﺽ. ﻓﺎﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ
ﺑﻐﻴﺮ ﻋﻮﺽ ﻓﺘﺠﻮﺯ ﻣﻄﻠﻘﺎ ﻣﻦ
ﻏﻴﺮ ﺗﻘﻴﻴﺪ ﺑﺸﻲﺀ ﻣﻌﻴﻦ،
ﻛﺎﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ ﻋﻠﻰ ﺍﻻﻗﺪﺍﻡ،
ﻭﺍﻟﺴﻔﻦ، ﻭﺍﻟﻄﻴﻮﺭ، ﻭﺍﻟﺒﻐﺎﻝ،
ﻭﺍﻟﺤﻤﺮ، ﻭﺍﻟﻤﺰﺍﺭﻳﻖ،
ﻭﺍﻟﻤﺼﺎﺭﻋﺔ، ﻭﺭﻓﻊ ﺍﻟﺤﺠﺮ
ﻟﻴﻌﺮﻑ ﺍﻻﺷﺪ، ﻭﻏﻴﺮ ﺫﻟﻚ؛ ﻻﻥ
ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻛﺎﻥ
ﻓﻲ ﺳﻔﺮ ﻣﻊ ﻋﺎﺋﺸﺔ ﻓﺴﺎﺑﻘﺘﻪ
ﻋﻠﻰ ﺭﺟﻠﻬﺎ، ﻓﺴﺒﻘﺘﻪ، ﻗﺎﻟﺖ: ﻓﻠﻤﺎ
ﺣﻤﻠﺖ ﺍﻟﻠﺤﻢ ﺳﺎﺑﻘﺘﻪ ﻓﺴﺒﻘﻨﻲ،
ﻓﻘﺎﻝ: ﻫﺬﻩ ﺑﺘﻠﻚ. ﺭﻭﺍﻩ ﺍﺑﻮﺩﺍﻭﺩ .
ﻭﺳﺎﺑﻖ ﺳﻠﻤﺔ ﺑﻦ ﺍﻻﻛﻮﻉ ﺭﺟﻼ
ﻣﻦ ﺍﻻﻧﺼﺎﺭ ﺑﻴﻦ ﻳﺪﻱ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ
ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻓﻲ ﻳﻮﻡ ﺫﻱ
ﻗﺮﺩ. ﻭﺻﺎﺭﻉ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺭﻛﺎﻧﺔ ﻓﺼﺮﻋﻪ. ﺭﻭﺍﻩ
ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ. ﻭﻣﺮ ﺑﻘﻮﻡ ﻳﺮﺑﻌﻮﻥ
ﺣﺠﺮﺍ ﻳﻌﻨﻲ ﻳﺮﻓﻌﻮﻧﻪ ﻟﻴﻌﺮﻓﻮﺍ
ﺍﻻﺷﺪ ﻣﻨﻬﻢ ﻓﻠﻢ ﻳﻨﻜﺮ ﻋﻠﻴﻬﻢ .
ﻭﺳﺎﺋﺮ ﺍﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺎﺕ ﻳﻘﺎﺱ ﻋﻠﻰ
ﻫﺬﺍ.{ ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Musabaka halal
ce cikin sunnar Manzon
Allah, da Ijma’in Maluma. A
cikin Sunnah dai Ibnu
Umar ya ruwaito cewa
Annabi mai tsira da
amincin Allah ya shirya
Musabaka tsakanin
dawakin da aka yi musu
“Tadhmiir” (watau
wadanda aka yi musu
horon tinkarar yaki ta
hanyar karanta abinci gare
su da sanya musu
tufafinsu da sauransu) a
filin da ya taso daga
Haifaa har zuwa
Thaniyyatul Wadaa, haka
nan ya shirya wata
Musabakar tsakanin
dawakin da ba a yi musu
Tadhmiiri ba, a filin da ya
taso daga Thaniyyatul
Wadaa har zuwa Masjidu
Bani Zuraiq. Buhari da
Muslim ne suka ruwaito
hadithin…Sannan Musulmi
sun yi Ijma’i a kan halaccin
Musabaka a dunkule.
Sannan ita Musabaka ta
kasu ne zuwa kashi biyu:
Musabaka da ake yi tare
da sanya wasu kudi cikinta
(ga duk wanda ya yi
nasara). Akwai kuma
Musabaka da ake yi ba
tare da an sanya kudi
cikinta (ga duk wanda ya
yi nasara ba). To ita
Musabaka da ake yi ba
tare da an sanya wasu
kudi cikinta ba wannan ta
halatta ba tare da sanya
mata wani tarnaki a
cikinta ba, kamar dai
Musabakar da ake yi na
tseren gudu da kafa, ko
Musabakar tseren jiragen
ruwa, ko Musabakar tsere
tsakanin tsutsaye, ko
Musabakar tsere tsakanin
alfadaru, ko Musabakar
tsere tsakanin jakuna, ko
Musabakar tsere tsakanin
giwaye, ko Musabakar yin
harbi da kananan masu,
ko Musabakar yin kokowa,
ko Musabakar daga dutse
mai nauyi sanoda gwada
karfi, da dai nau’o’in
Musabaka dabam daban.
Saboda Annbi mai tsira da
amincin Allah wata rana a
hanyar tafiye-tafiyensa ya
yi Musabakar tseren gudu
da kafa tsakaninsa da
matarsa Nana A’isha Allah
Ya kara mata yarda, kuma
ta yi nasara a kansa. Sai
A’isha ta ce: da na yi kiba
sai wata rana muka sake
yin Musabakar tseren
gudu da kafa sai ya yi
nasara a kaina. Sai ya ce
da ni: ni ma na rama
wancan ci da kika yi mini.
Wannan hadithi Abu
Dawuda ne ya ruwaito shi.
Kuma Salamah Dan Ak’wa
ya yi Musabakar tsere da
kafa tsakaninsa da wani
mutum a gaban Annabi
mai tsira da amincin Allah
a ranar Ruwan Zuu Qarad.
Sannan Annabi mai tsira
da amincin Allah ya yi
Musabakar kokowa
tsakaninsa da wani
gwanin kokowa mai suna
Rukaanah, kuma ya yi
nasara a kansa ya kada
shi. Tirmizii ne ya ruwaito
hafithin. Sannan wata rana
Annabi mai tsira da
amincin Allah ya wuce
wasu mutane suna
Musabakar daga dutse mai
nauyi saboda sanin wane
ne ya fi karfi, amma bai
hana su yin hakan ba.
Sauran Musabakpkin sai a
kiyasta su a kan
wadannan)) [da nassi ya
tabbatar]. Intaha.
2. Imamu Ibnu Qayyimil
Jauziyyah wanda ya mutu
a shekarar Hijira ta 751
watau yau shekaru 684 ke
nan da suka wuce ya ce
cikin littafinsa mai suna
Alfuruusiyyah 1/318:-
{ ﺍﻟﻤﺴﺎﻟﺔ ﺍﻟﺤﺎﺩﻳﺔ ﻋﺸﺮﺓ:
ﺍﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ ﻋﻠﻰ ﺣﻔﻆ ﺍﻟﻘﺮﺍﻥ،
ﻭﺍﻟﺤﺪﻳﺚ، ﻭﺍﻟﻔﻘﻪ، ﻭﻏﻴﺮﻩ ﻣﻦ
ﺍﻟﻌﻠﻮﻡ ﺍﻟﻨﺎﻓﻌﺔ، ﻭﺍﻻﺻﺎﺑﺔ ﻓﻲ
ﺍﻟﻤﺴﺎﺋﻞ، ﻫﻞ ﺗﺠﻮﺯ ﺑﻌﻮﺽ؟
ﻣﻨﻌﻪ ﺍﺻﺤﺎﺏ ﻣﺎﻟﻚ، ﻭﺍﺣﻤﺪ،
ﻭﺍﻟﺸﺎﻓﻌﻲ. ﻭﺟﻮﺯﻩ ﺍﺻﺤﺎﺏ ﺍﺑﻲ
ﺣﻨﻴﻔﺔ، ﻭﺷﻴﺨﻨﺎ، ﻭﺣﻜﺎﻩ ﺍﺑﻦ ﻋﺒﺪ
ﺍﻟﺒﺮ ﻋﻦ ﺍﻟﺸﺎﻓﻌﻲ. ﻭﻫﻮ ﺍﻭﻟﻰ
ﻣﻦ ﺍﻟﺸﺒﺎﻙ، ﻭﺍﻟﺼﺮﺍﻉ،
ﻭﺍﻟﺴﺒﺎﺣﺔ، ﻓﻤﻦ ﺟﻮﺯ ﺍﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ
ﻋﻠﻴﻬﺎ ﺑﻌﻮﺽ، ﻓﺎﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ ﻋﻠﻰ
ﺍﻟﻌﻠﻢ ﺍﻭﻟﻰ ﺑﺎﻟﺠﻮﺍﺯ، ﻭﻫﻲ
ﺻﻮﺭﺓ ﻣﺮﺍﻫﻨﺔ ﺍﻟﺼﺪﻳﻖ ﻟﻜﻔﺎﺭ
ﻗﺮﻳﺶ ﻋﻠﻰ ﺻﺤﺔ ﻣﺎ ﺍﺧﺒﺮﻫﻢ
ﺑﻪ، ﻭﺛﺒﻮﺗﻪ. ﻭﻗﺪ ﺗﻘﺪﻡ ﺍﻧﻪ ﻟﻢ
ﻳﻘﻢ ﺩﻟﻴﻞ ﺷﺮﻋﻲ ﻋﻠﻰ ﻧﺴﺨﻪ .
ﻭﺍﻥ ﺍﻟﺼﺪﻳﻖ ﺍﺧﺬ ﺭﻫﻨﻬﻢ ﺑﻌﺪ
ﺗﺤﺮﻳﻢ ﺍﻟﻘﻤﺎﺭ. ﻭﺍﻥ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﻗﻴﺎﻣﻪ
ﺑﺎﻟﺤﺠﺔ، ﻭﺍﻟﺠﻬﺎﺩ، ﻓﺎﺫﺍ ﺟﺎﺯﺕ
ﺍﻟﻤﺮﺍﻫﻨﺔ ﻋﻠﻰ ﺍﻻﺕ ﺍﻟﺠﻬﺎﺩ،
ﻓﻬﻲ ﻓﻲ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﺍﻭﻟﻰ ﺑﺎﻟﺠﻮﺍﺯ.
ﻭﻫﺬﺍ ﺍﻟﻘﻮﻝ ﻫﻮ ﺍﻟﺮﺍﺟﺢ.{ ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Mas’alah ta
goma sha daya: Yin
Musabakar haddace
Alkur’ani, da Hadithi, da
Fiqhu, da wasu
Ilmummuka masu amfani,
ko gane abin da yake
daidai cikin wasu
mas’alolin, shirya irin
wannan Musabaka a bisa
wani kudi, shin hakan zai
halatta ko kuwa ba zai
halatta ba? Mutanen Malik,
da Ahmad, da Sha’fi’ii sun
hana yin sa. Amma
mutanen Abu Hanifah da
Malaminmu (Ibnu
Taimiyah) da ma hikayar
Ibnu Abdil Barr daga
Sha’fi’ii sun halatta yinsa.
Shi wannan nau’i na
Musabaka ya fi yin
Musabaka a kan harkar iya
sa tarko, ko kokowa, ko
ninkaya, sanoda haka
wadanda suka halatta
shirya Musabaka a bisa
kudi cikin wadannan, lalle
shirya Musabaka cikin
harkokin habaka ilmi shi
zai fi cancantar halatta,
kuma wannan ita ce surar
Muraahanar da Sbubakar
Siddiq ya yi da kafuran
Quraishawa a kan gaskiyar
labarin da ya ba su (na
cewa Ruumaawa za su yi
nasara a kan Faatisaawa
bayan shekaru kadan).
Dalili ya gabata na cewa
babu abin da ya shafe
ingancin wannan
Muraahanar. Kuma shi
Abubakar ya yi
Muraahanar da su ne
bayan haramta yin caca.
Sannan ita tsayuwar
Addini da ma tana
samuwa ne ta hanyar kafa
hujja, da yin jihadi, saboda
wannan idan har
Muraahanah za ta halatta
a kan abubuwan karfafa
jihadi, ke nan ta halatta a
kan abubuwan karfafa ilmi
da za su karfafa kafa hujja
shi ne zai fi cancanta,
kuma wannan magana ita
ce abin rinjayarwa)).
Intaha.
***************
***************
Lalle da wadannan
bayanai ne mahankalta za
su fahimci cewa ita
Musabakar haddar
Alkur’ani mai girma, ko
musabakar haddar
Hadithan Manzon Allah
Masu daraja, ko
musabakar haddar wani
ilmi mai amfani -tare da
sanya wani kudi ga wanda
ya yi nasara ko kuwa ba
tare da sanya wani kudi
ga wanda ya yi nasara ba-
abu ne da yake halal ta
hanyar hujjoji biyu:-
1. Ijma’i.
2. Qiyaasi.
Wannan kuwa duka
sabanin maida ranar
haihuwar Annabi mai tsira
da amincin Allah wani Idi
ne, wanda babu Ijma’i a
kansa, babu kuma wani
Qiyaasi sahihi a kansa.
Muna rokon Allah Ya
taimake mu Ya tabbatar
da dugaduganmu a kan
Sunnar Annabi mai tsira da
amincin Allah. Ameen.
Sheikh Dr. Ibrahim Jalo
Jalingo
(Chairman Council of
Ulama’u, Jibwis Nigeria )
09/Rabi Rabi – Al
Awwal/1436.
29/December/2014. —

Advertisements

MUSABAKAR HADDAR ALQUR’ANI KO HADITHI KO WANI NAU’IN ILMI A MAHANGAR MUSULUNCI:

Aside

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out / Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out / Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out / Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out / Change )

Connecting to %s

Dr. Ibrahim Jalo Jalingo, SUNNAH

MUSABAKAR HADDAR
ALQUR’ANI KO HADITHI KO
WANI NAU’IN ILMI A
MAHANGAR MUSULUNCI:
Da yawa daga cikin
wadanda suka zaba wa
kansu sabanin shiriyar
Manzon Allah cikin
gudanar da addininsu
suna ganin cewa: In har
Idin Maulidi bidi’ah ne, to
kuwa lalle Musabaka a kan
haddar Alqur’ani Mai
girma, ko haddar Hadithan
Annabi masu daraja ko
haddar wani ilmi na
Musulunci su ma yin su
bidi’ah ce!!!
***************
**********
A nan muna ganin cewa
yawan nisantar wadannan
mutane ga littattafan
Shari’ah na maluman
Musulunci ne ya sa ba su
ma san cewa: Dukkan abin
da halaccinsa ya tabbata
ta yanyar Ijma’in Musulmi
cikin wani zamani daga
cikin zamuna, to dole ne
ya zamanto daya daga
cikin abubuwa uku:-
1- ko dai ya zamanto
Mubaahi, watau abin da
yin sa da rashin yin sa duk
daya a idanun Shari’ah.
2- ko kuwa ya zamanto
Mustahabbi, watau abin
da in har ba a yi shi ba to
ba a yi wani laifi ba, in
kuma aka yi shi to ana da
wani lada na musamman.
3- ko kuwa ya zamanto
Waajibi, watau abin da in
har ba a yi shi ba za a sami
zunubi, in kuma an yi shi
to an yi abin da Shari’ah ta
tilasta yin shi.
***************
***************
shi kuwa Musabaka domin
haddar Alqur’ani Mai
girma abu ne da Maluman
Sunnah, da su kansu masu
bidi’ah na Duniya suka
hadu a kan halaccinsa a
bisa hujjar kiyasin shi a
kan Musaabakokin da
Nassi ya zo da halaccinsu.
In kuwa haka lamarin
yake, to ta kaka ne za a
hada hukuncin Musaabaka
domin haddar Alqur’ani da
hukuncin Idin Maulidin da
babu mai yin shi ko
halatta shi in banda wasu
daga cikin masu yin
bidi’ah??
*********************
HUKUNCIN MUSABAKA:
1. Imam Ibnu Qudaamah
mai rasuwa a shekara ta
620 watau da mutuwarsa
yau shekaru 815 ke nan,
ya ce cikin littafinsa mai
suna Almugnii
13/404-405 :-
{ ﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ ﺟﺎﺋﺰﺓ ﺑﺎﻟﺴﻨﺔ
ﻭﺍﻻﺟﻤﺎﻉ، ﺍﻣﺎ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﻓﺮﻭﻯ ﺍﺑﻦ
ﻋﻤﺮ ﺍﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ
ﻭﺳﻠﻢ ﺳﺎﺑﻖ ﺑﻴﻦ ﺍﻟﺨﻴﻞ
ﺍﻟﻤﻀﻤﺮﺓ ﻣﻦ ﺍﻟﺤﻔﻴﺎﺀ ﺍﻟﻰ ﺛﻨﻴﺔ
ﺍﻟﻮﺩﺍﻉ، ﻭﺑﻴﻦ ﺍﻟﺘﻲ ﻟﻢ ﺗﻀﻤﺮ ﻣﻦ
ﺛﻨﻴﺔ ﺍﻟﻮﺩﺍﻉ ﺍﻟﻰ ﻣﺴﺠﺪ ﺑﻨﻲ
ﺯﺭﻳﻖ. ﻣﺘﻔﻖ ﻋﻠﻴﻪ… ﻭﺍﺟﻤﻊ
ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻮﻥ ﻋﻠﻰ ﺟﻮﺍﺯ ﺍﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ
ﻓﻲ ﺍﻟﺠﻤﻠﺔ. ﻭﺍﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ ﻋﻠﻰ
ﺿﺮﺑﻴﻦ: ﻣﺴﺎﺑﻘﺔ ﺑﻐﻴﺮ ﻋﻮﺽ،
ﻭﻣﺴﺎﺑﻘﺔ ﺑﻌﻮﺽ. ﻓﺎﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ
ﺑﻐﻴﺮ ﻋﻮﺽ ﻓﺘﺠﻮﺯ ﻣﻄﻠﻘﺎ ﻣﻦ
ﻏﻴﺮ ﺗﻘﻴﻴﺪ ﺑﺸﻲﺀ ﻣﻌﻴﻦ،
ﻛﺎﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ ﻋﻠﻰ ﺍﻻﻗﺪﺍﻡ،
ﻭﺍﻟﺴﻔﻦ، ﻭﺍﻟﻄﻴﻮﺭ، ﻭﺍﻟﺒﻐﺎﻝ،
ﻭﺍﻟﺤﻤﺮ، ﻭﺍﻟﻤﺰﺍﺭﻳﻖ،
ﻭﺍﻟﻤﺼﺎﺭﻋﺔ، ﻭﺭﻓﻊ ﺍﻟﺤﺠﺮ
ﻟﻴﻌﺮﻑ ﺍﻻﺷﺪ، ﻭﻏﻴﺮ ﺫﻟﻚ؛ ﻻﻥ
ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻛﺎﻥ
ﻓﻲ ﺳﻔﺮ ﻣﻊ ﻋﺎﺋﺸﺔ ﻓﺴﺎﺑﻘﺘﻪ
ﻋﻠﻰ ﺭﺟﻠﻬﺎ، ﻓﺴﺒﻘﺘﻪ، ﻗﺎﻟﺖ: ﻓﻠﻤﺎ
ﺣﻤﻠﺖ ﺍﻟﻠﺤﻢ ﺳﺎﺑﻘﺘﻪ ﻓﺴﺒﻘﻨﻲ،
ﻓﻘﺎﻝ: ﻫﺬﻩ ﺑﺘﻠﻚ. ﺭﻭﺍﻩ ﺍﺑﻮﺩﺍﻭﺩ .
ﻭﺳﺎﺑﻖ ﺳﻠﻤﺔ ﺑﻦ ﺍﻻﻛﻮﻉ ﺭﺟﻼ
ﻣﻦ ﺍﻻﻧﺼﺎﺭ ﺑﻴﻦ ﻳﺪﻱ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ
ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻓﻲ ﻳﻮﻡ ﺫﻱ
ﻗﺮﺩ. ﻭﺻﺎﺭﻉ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺭﻛﺎﻧﺔ ﻓﺼﺮﻋﻪ. ﺭﻭﺍﻩ
ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ. ﻭﻣﺮ ﺑﻘﻮﻡ ﻳﺮﺑﻌﻮﻥ
ﺣﺠﺮﺍ ﻳﻌﻨﻲ ﻳﺮﻓﻌﻮﻧﻪ ﻟﻴﻌﺮﻓﻮﺍ
ﺍﻻﺷﺪ ﻣﻨﻬﻢ ﻓﻠﻢ ﻳﻨﻜﺮ ﻋﻠﻴﻬﻢ .
ﻭﺳﺎﺋﺮ ﺍﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺎﺕ ﻳﻘﺎﺱ ﻋﻠﻰ
ﻫﺬﺍ.{ ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Musabaka halal
ce cikin sunnar Manzon
Allah, da Ijma’in Maluma. A
cikin Sunnah dai Ibnu
Umar ya ruwaito cewa
Annabi mai tsira da
amincin Allah ya shirya
Musabaka tsakanin
dawakin da aka yi musu
“Tadhmiir” (watau
wadanda aka yi musu
horon tinkarar yaki ta
hanyar karanta abinci gare
su da sanya musu
tufafinsu da sauransu) a
filin da ya taso daga
Haifaa har zuwa
Thaniyyatul Wadaa, haka
nan ya shirya wata
Musabakar tsakanin
dawakin da ba a yi musu
Tadhmiiri ba, a filin da ya
taso daga Thaniyyatul
Wadaa har zuwa Masjidu
Bani Zuraiq. Buhari da
Muslim ne suka ruwaito
hadithin…Sannan Musulmi
sun yi Ijma’i a kan halaccin
Musabaka a dunkule.
Sannan ita Musabaka ta
kasu ne zuwa kashi biyu:
Musabaka da ake yi tare
da sanya wasu kudi cikinta
(ga duk wanda ya yi
nasara). Akwai kuma
Musabaka da ake yi ba
tare da an sanya kudi
cikinta (ga duk wanda ya
yi nasara ba). To ita
Musabaka da ake yi ba
tare da an sanya wasu
kudi cikinta ba wannan ta
halatta ba tare da sanya
mata wani tarnaki a
cikinta ba, kamar dai
Musabakar da ake yi na
tseren gudu da kafa, ko
Musabakar tseren jiragen
ruwa, ko Musabakar tsere
tsakanin tsutsaye, ko
Musabakar tsere tsakanin
alfadaru, ko Musabakar
tsere tsakanin jakuna, ko
Musabakar tsere tsakanin
giwaye, ko Musabakar yin
harbi da kananan masu,
ko Musabakar yin kokowa,
ko Musabakar daga dutse
mai nauyi sanoda gwada
karfi, da dai nau’o’in
Musabaka dabam daban.
Saboda Annbi mai tsira da
amincin Allah wata rana a
hanyar tafiye-tafiyensa ya
yi Musabakar tseren gudu
da kafa tsakaninsa da
matarsa Nana A’isha Allah
Ya kara mata yarda, kuma
ta yi nasara a kansa. Sai
A’isha ta ce: da na yi kiba
sai wata rana muka sake
yin Musabakar tseren
gudu da kafa sai ya yi
nasara a kaina. Sai ya ce
da ni: ni ma na rama
wancan ci da kika yi mini.
Wannan hadithi Abu
Dawuda ne ya ruwaito shi.
Kuma Salamah Dan Ak’wa
ya yi Musabakar tsere da
kafa tsakaninsa da wani
mutum a gaban Annabi
mai tsira da amincin Allah
a ranar Ruwan Zuu Qarad.
Sannan Annabi mai tsira
da amincin Allah ya yi
Musabakar kokowa
tsakaninsa da wani
gwanin kokowa mai suna
Rukaanah, kuma ya yi
nasara a kansa ya kada
shi. Tirmizii ne ya ruwaito
hafithin. Sannan wata rana
Annabi mai tsira da
amincin Allah ya wuce
wasu mutane suna
Musabakar daga dutse mai
nauyi saboda sanin wane
ne ya fi karfi, amma bai
hana su yin hakan ba.
Sauran Musabakpkin sai a
kiyasta su a kan
wadannan)) [da nassi ya
tabbatar]. Intaha.
2. Imamu Ibnu Qayyimil
Jauziyyah wanda ya mutu
a shekarar Hijira ta 751
watau yau shekaru 684 ke
nan da suka wuce ya ce
cikin littafinsa mai suna
Alfuruusiyyah 1/318:-
{ ﺍﻟﻤﺴﺎﻟﺔ ﺍﻟﺤﺎﺩﻳﺔ ﻋﺸﺮﺓ:
ﺍﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ ﻋﻠﻰ ﺣﻔﻆ ﺍﻟﻘﺮﺍﻥ،
ﻭﺍﻟﺤﺪﻳﺚ، ﻭﺍﻟﻔﻘﻪ، ﻭﻏﻴﺮﻩ ﻣﻦ
ﺍﻟﻌﻠﻮﻡ ﺍﻟﻨﺎﻓﻌﺔ، ﻭﺍﻻﺻﺎﺑﺔ ﻓﻲ
ﺍﻟﻤﺴﺎﺋﻞ، ﻫﻞ ﺗﺠﻮﺯ ﺑﻌﻮﺽ؟
ﻣﻨﻌﻪ ﺍﺻﺤﺎﺏ ﻣﺎﻟﻚ، ﻭﺍﺣﻤﺪ،
ﻭﺍﻟﺸﺎﻓﻌﻲ. ﻭﺟﻮﺯﻩ ﺍﺻﺤﺎﺏ ﺍﺑﻲ
ﺣﻨﻴﻔﺔ، ﻭﺷﻴﺨﻨﺎ، ﻭﺣﻜﺎﻩ ﺍﺑﻦ ﻋﺒﺪ
ﺍﻟﺒﺮ ﻋﻦ ﺍﻟﺸﺎﻓﻌﻲ. ﻭﻫﻮ ﺍﻭﻟﻰ
ﻣﻦ ﺍﻟﺸﺒﺎﻙ، ﻭﺍﻟﺼﺮﺍﻉ،
ﻭﺍﻟﺴﺒﺎﺣﺔ، ﻓﻤﻦ ﺟﻮﺯ ﺍﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ
ﻋﻠﻴﻬﺎ ﺑﻌﻮﺽ، ﻓﺎﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ ﻋﻠﻰ
ﺍﻟﻌﻠﻢ ﺍﻭﻟﻰ ﺑﺎﻟﺠﻮﺍﺯ، ﻭﻫﻲ
ﺻﻮﺭﺓ ﻣﺮﺍﻫﻨﺔ ﺍﻟﺼﺪﻳﻖ ﻟﻜﻔﺎﺭ
ﻗﺮﻳﺶ ﻋﻠﻰ ﺻﺤﺔ ﻣﺎ ﺍﺧﺒﺮﻫﻢ
ﺑﻪ، ﻭﺛﺒﻮﺗﻪ. ﻭﻗﺪ ﺗﻘﺪﻡ ﺍﻧﻪ ﻟﻢ
ﻳﻘﻢ ﺩﻟﻴﻞ ﺷﺮﻋﻲ ﻋﻠﻰ ﻧﺴﺨﻪ .
ﻭﺍﻥ ﺍﻟﺼﺪﻳﻖ ﺍﺧﺬ ﺭﻫﻨﻬﻢ ﺑﻌﺪ
ﺗﺤﺮﻳﻢ ﺍﻟﻘﻤﺎﺭ. ﻭﺍﻥ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﻗﻴﺎﻣﻪ
ﺑﺎﻟﺤﺠﺔ، ﻭﺍﻟﺠﻬﺎﺩ، ﻓﺎﺫﺍ ﺟﺎﺯﺕ
ﺍﻟﻤﺮﺍﻫﻨﺔ ﻋﻠﻰ ﺍﻻﺕ ﺍﻟﺠﻬﺎﺩ،
ﻓﻬﻲ ﻓﻲ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﺍﻭﻟﻰ ﺑﺎﻟﺠﻮﺍﺯ.
ﻭﻫﺬﺍ ﺍﻟﻘﻮﻝ ﻫﻮ ﺍﻟﺮﺍﺟﺢ.{ ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Mas’alah ta
goma sha daya: Yin
Musabakar haddace
Alkur’ani, da Hadithi, da
Fiqhu, da wasu
Ilmummuka masu amfani,
ko gane abin da yake
daidai cikin wasu
mas’alolin, shirya irin
wannan Musabaka a bisa
wani kudi, shin hakan zai
halatta ko kuwa ba zai
halatta ba? Mutanen Malik,
da Ahmad, da Sha’fi’ii sun
hana yin sa. Amma
mutanen Abu Hanifah da
Malaminmu (Ibnu
Taimiyah) da ma hikayar
Ibnu Abdil Barr daga
Sha’fi’ii sun halatta yinsa.
Shi wannan nau’i na
Musabaka ya fi yin
Musabaka a kan harkar iya
sa tarko, ko kokowa, ko
ninkaya, sanoda haka
wadanda suka halatta
shirya Musabaka a bisa
kudi cikin wadannan, lalle
shirya Musabaka cikin
harkokin habaka ilmi shi
zai fi cancantar halatta,
kuma wannan ita ce surar
Muraahanar da Sbubakar
Siddiq ya yi da kafuran
Quraishawa a kan gaskiyar
labarin da ya ba su (na
cewa Ruumaawa za su yi
nasara a kan Faatisaawa
bayan shekaru kadan).
Dalili ya gabata na cewa
babu abin da ya shafe
ingancin wannan
Muraahanar. Kuma shi
Abubakar ya yi
Muraahanar da su ne
bayan haramta yin caca.
Sannan ita tsayuwar
Addini da ma tana
samuwa ne ta hanyar kafa
hujja, da yin jihadi, saboda
wannan idan har
Muraahanah za ta halatta
a kan abubuwan karfafa
jihadi, ke nan ta halatta a
kan abubuwan karfafa ilmi
da za su karfafa kafa hujja
shi ne zai fi cancanta,
kuma wannan magana ita
ce abin rinjayarwa)).
Intaha.
***************
***************
Lalle da wadannan
bayanai ne mahankalta za
su fahimci cewa ita
Musabakar haddar
Alkur’ani mai girma, ko
musabakar haddar
Hadithan Manzon Allah
Masu daraja, ko
musabakar haddar wani
ilmi mai amfani -tare da
sanya wani kudi ga wanda
ya yi nasara ko kuwa ba
tare da sanya wani kudi
ga wanda ya yi nasara ba-
abu ne da yake halal ta
hanyar hujjoji biyu:-
1. Ijma’i.
2. Qiyaasi.
Wannan kuwa duka
sabanin maida ranar
haihuwar Annabi mai tsira
da amincin Allah wani Idi
ne, wanda babu Ijma’i a
kansa, babu kuma wani
Qiyaasi sahihi a kansa.
Muna rokon Allah Ya
taimake mu Ya tabbatar
da dugaduganmu a kan
Sunnar Annabi mai tsira da
amincin Allah. Ameen.
Sheikh Dr. Ibrahim Jalo
Jalingo
(Chairman Council of
Ulama’u, Jibwis Nigeria )
09/Rabi Rabi – Al
Awwal/1436.
29/December/2014. —

MUSABAKAR HADDAR ALQUR’ANI KO HADITHI KO WANI NAU’IN ILMI A MAHANGAR MUSULUNCI:

Aside

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out / Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out / Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out / Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out / Change )

Connecting to %s