SUNNAH

Muhimman Shafukan
Gidajen Yanar Gizo domin
karuwar Musulmai
Yanar gizo (Internet) a
wannan zamani ta zama
abokiyar rayuwa, wanda
masu amfani da ita ba
zasu iya koda kwana
daya ba tare da sun kai
ziyara ba, sai dai da wani
kwakkwaran dalili, kamar
rashin lafiya ko rashin
service. A wani bincike da
masana suka gabatar a
wannan zamani jama’a
sunfi cinye lokacinsu a
wurin amfani da Yanar
Gizo sama da komai.
Wasu na cinye lokacin
nasu a bincike bincike da
kalle kalle marar amfani,
wasu kuma basu da aiki
sai neman abokan hira
daga sassan duniya
daban – daban, wasu
kuma Allah ya taimake
su, suna cinye lokacin
nasu ne akan karin
neman ilimi, musamman
ilimin addinin Musulunci.
Ga duk masu sha’awar
amfanar lokacin a
duniyar yanar gizo ga
shafuka masu
muhimmanci domin
Musulunci da Musulmai:-
Islami City (http://
http://www.islamicity.com) –
shafi ne daya kunshi
abubuwa masu yawan
gaske kamarsu bayani
game da Shika-shikan
Musulunci, Lokutan sallah,
litattafai da sauransu.
Qur’an Complex (http://
http://www.qurancomplex.org)
– shafi ne da tsohon
sarkin kasar Saudi Arabia
King Fahaq bin Abdallah
ya samar dashi game da
Al Qur’an Mai girma.
Fatwa Islam (http://
http://www.fatwaislam.com) –
shafi ne dake cike da
fatawoyin manya
manyan Malam na da
dana yanzu. Sannan
kuma mutum zai iya tura
fatawarsa a dawo masa
da amsa nan take.
Islam Online (http://
http://www.islamonline.com) –
wannan shafi ne daya
danganci bangaren
labarun abubuwan dake
faruwa a duniyar
Musulunci. Sai kuma hira
ta keke da keke (Video
Chat) tsakanin Musulmai
dake sassan duniya
daban – daban.
Islam Question & Answer
(http://islamqa.com) –
shafi ne dake kunshe da
tambayoyi da
amsoshinsu dangane da
abubuwan da suka
shigewa Musulmai duhu.
Ja’afa Mahmud Adam
(http://www.
jaafarmahmudadam.org)
– wannan shafin na
kunshe da wa’azin
Marigayi Malam Ja’afar
Mahmud Adam da kuma
fatawoyinsa.
Haruna Yahya (http://
http://www.harunyahya.com) –
Shafin haziki kuma fasihi
Harun Yahya wannan
yake bayani game da
kimiya da fahasa, a
mahangar Musulunci.
Idan kuma mutum yana
neman wani abu bai
samu ba, a cikin
wadannan shafuka dake
sama zai iya ziyarta
shafin bincike na Google
don bincikowa. Allah ya
kara taimakon addinin
Musulunci da Musulmai
baki daya.
Bashir Ahmad
bashirgy@yahoo.com
08032493020

Advertisements

Muhimman Shafukan Gidajen Yanar Gizo domin karuwar Musulmai

Aside
SUNNAH

SANYA TUFAFI YAWUCE
IDON ‘KAFA HARAMUNNE
KUMA ALLAAH YAYIWA
MA’ABOCINSA TANADIN
AZABA MAI RA’DA’DI.
Yana daga abunda
yazama ruwan dare
gama-duniya har yazama
an maidashi kamar ba laifi
ba; shine sanya tufafin da
yawuce idon sawu(‘kafa)
ga maza.
A inda zakaga babba da
yaro, mahaifa da ‘ya’ya,
malamai da dalibai, masu
kudi da talakawa, suna
sanya tufafi(riga ko wando
ko malum-malum) ‘kasa
da idon sawu.
Bayan kuma yin hakan
haramunne qa’d’an, kamar
yadda hakan ya tabbata
daga fiyayyen halitta
(s.a.w) kuma hadisan sun
bayyana narkon azaba
mai ra’da’di da ‘kuna ga
duk mai aikata hakan.
Ga wadannan hadisan
kamar haka:
– ﺭﻭﻯ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﻋﻦ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ
ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺁﻟﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺃﻧﻪ ﻗﺎﻝ :
) ﻣﺎ ﺃﺳﻔﻞ ﻣﻦ ﺍﻟﻜﻌﺒﻴﻦ ﻣﻦ
ﺍﻹﺯﺍﺭ ﻓﻔﻲ ﺍﻟﻨﺎﺭ ( ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﺭﻗﻢ
5787.
Ma’ana: Duk tufafin da
yawuce idon ‘kafa
ma’abocinsa dan wutane.
ﻭﻗﺎﻝ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺁﻟﻪ ﻭﺳﻠﻢ
) ﺛَﻠَﺎﺛَﺔٌ ﻟَﺎ ﻳُﻜَﻠِّﻤُﻬُﻢُ ﺍﻟﻠﻪُ ﻳَﻮْﻡَ
ﺍﻟْﻘِﻴَﺎﻣَﺔِ، ﻭَﻟَﺎ ﻳَﻨْﻈُﺮُ ﺇِﻟَﻴْﻬِﻢْ ﻭَﻟَﺎ
ﻳُﺰَﻛِّﻴﻬِﻢْ ﻭَﻟَﻬُﻢْ ﻋَﺬَﺍﺏٌ ﺃَﻟِﻴﻢٌ:
ﺍﻟْﻤُﺴْﺒِﻞُ، ﻭَﺍﻟْﻤَﻨَّﺎﻥُ، ﻭَﺍﻟْﻤُﻨَﻔِّﻖُ
ﺳِﻠْﻌَﺘَﻪُ ﺑِﺎﻟْﺤَﻠِﻒِ ﺍﻟْﻜَﺎﺫِﺏِ « ( ﺭﻭﺍﻩ
ﻣﺴﻠﻢ ﺭﻗﻢ 106
Ma’ana: Mutane guda uku
idan aka tashi ranar
alkiyama Allaah bazaiyi
magana dasu ba, bazai
kallesu ba, bazai
tsarkakesu ba, kuma suna
da azaba mai ra’da’di,
sune: Wanda tufafinsa ya
wuce idon ‘kafa,
Annamimi, mai yawan
rantsuwar akan ‘karya
wurin siyar da hajarsa.
ﻭﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﺳﻌﻴﺪ ﺍﻟﺨﺪﺭﻱ ﺭﺿﻲ
ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﺃﻧﻪ ﻗﺎﻝ: ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ
ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺁﻟﻪ ﻭﺳﻠﻢ:
) ﺇﺯﺭﺓ ﺍﻟﻤﺴﻠﻢ ﺇﻟﻰ ﻧﺼﻒ ﺍﻟﺴﺎﻕ
ﻭﻻ ﺣﺮﺝ ﻭﻻ ﺟﻨﺎﺡ ﻓﻴﻤﺎ ﺑﻴﻨﻪ ﻭﺑﻴﻦ
ﺍﻟﻜﻌﺒﻴﻦ ، ﻭﻣﺎ ﻛﺎﻥ ﺃﺳﻔﻞ ﻣﻦ
ﺍﻟﻜﻌﺒﻴﻦ ﻓﻬﻮ ﻓﻲ ﺍﻟﻨﺎﺭ ( ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺑﻮ
ﺩﺍﻭﺩ ﻭﻫﻮ ﺛﺎﺑﺖ. ﺭﻗﻢ 4093 .
Ma’ana: Tufafin musulmi
zuwa rabin ‘kwaurine,
amma babu laifi ga
abunda ke tsakanin rabin
‘kwauri da idon ‘kafa,
kuma duk wanda yasanya
yawuce idon ‘kafa to ‘dan
wutane.
Wadannan hadisan da
makamantansu suna nuna
mana sanya tufafi daidai
rabin kwauri shi akafiso,
amma babu laifi idan
yazama tsakanin kwauri
da idon ‘kafa. Sannan
kuma sun bayyana mana
haramcin sanya tufafi kasa
da idon sawu, kuma duk
mai wannan dabi’ar Allaah
yayi mishi tanadin azaba
mai ra’da’di.
Amma a wadannan
zamunnan sai shai’dan
yayi galaba akan jama’a; a
inda zakaga mata na ‘dage
tufafinsu sukuma maza
suna takewa, Allaah
yakaremu daga fito na fito
da shari’arsa.
Sannan zakaga wasu suna
kawo shubuha akan cewa
su ba da girman kai suke
sawa ba, wanda wannan
yike nuna rashin
fahimtarsu ga hadisan,
domin hadisan dasukazo
da ‘kaidin sanya tufafi don
girman kai; sun bayyana
‘karin laifine da narkon
azaba ga mai aikata
hakan. Ma’ana bayan
sa’bon Allaah dakayi na
sanya tufafin da yawuce
idon sawu sai kuma
kahadashi dawani sa’bon
wanda yafishi muni; wato
girman kai da fankama da
ji-dakai. Domin Tirmizhiy
ya ruwiaito hadisi kuma
ya ingantantashi daga
sahabi Jabir yace: Manzon
Allaah yace masa:
( ﺇﻳّﺎﻙ ﻭﺇﺳﺒﺎﻝ ﺍﻹﺯﺍﺭ ﻓﺈﻧﻬـﺎ ﻣﻦ
ﺍﻟﻤﺨﻴﻠﺔ ﻭﺇﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻻ ﻳﺤﺐ
ﺍﻟﻤﺨﻴﻠﺔ ).
Ma’ana: Kada ka sanya
tufafinka yawuce idon
sawu, domin hakan yana
daga cikin girman kai,
kuma Allaah bayason
girman kai.
Sannan Ibn Hajr yana
cewa:
ﻭﻓﻲ ﻫﺬﻩ ﺍﻷﺣﺎﺩﻳﺚ: ﺃﻥ ﺇﺳﺒﺎﻝ
ﺍﻹﺯﺍﺭ ﻟﻠﺨﻴﻼﺀ ﻛﺒﻴﺮﺓ، ﻭﺃﻣﺎ
ﺍﻹﺳﺒﺎﻝ ﻟﻐﻴﺮ ﺍﻟﺨﻴﻼﺀ ﻓﻈﺎﻫﺮ
ﺍﻷﺣﺎﺩﻳﺚ ﺗﺤﺮﻳﻤﻪ ﺃﻳﻀﺎً .
Ma’ana: Wadannan
hadisan suna nuna mana
cewa sanya tufafi ‘kasa da
idon sawu da girman kai
babban kabirah ce, amma
sanyawa yawuce idon
sawu batare da girman kai
ba shi kuma haramunne.
ALLAAH YABAMU IKON
GYARAWA.
Dan’uwanku: Abdullahi
Almadeeniy kagarko.

SANYA TUFAFI YAWUCE IDON ‘KAFA HARAMUNNE KUMA ALLAAH YAYIWA MA’ABOCINSA TANADIN AZABA MAI RA’DA’DI.

Aside
Prof. Umar Labdo, SUNNAH

WURAREN DA AKE SAMUN
LITTAFANMU
.
By
Prof. Umar Labdo Muhammad
.
Saboda yawan tambaya
da makarantanmu suke yi,
muna ba da hakuri cewa a
yanzu ana samun mu kai
tsaye ne a Kano kawai.
Wannan shi ne a
cibiyarmu da kuke ganin
hotonta a kasa. Adireshin
shi ne: Unguwar Gommaja,
daura da gidan Malam
Aminu Kano (Mambayya
House), kusa da Dala
Maternity. Lambar waya:
08098653288.
Ana kuma samun littafan a
shagon Malam Ibrahim
Tsandari da shagon Malam
Ibrahim Dan Nijar, duka a
layin ‘yan littafi, Kasuwar
Kurmi, Kano.
Banda nan kuma, ana
samun littafan a duk inda
ake wa’azin Jama’atu
Izalatil Bid’ah wa Iqamatis
Sunnah (JIBWIS) na jiha ko
na kasa.
Don karin bayani, a
tuntubi lambar waya dake
sama.

WURAREN DA AKE SAMUN LITTAFAN Prof. Umar Labdo Muhammad

Aside
Uncategorized

By Dr. Ibrahim jalo jalingo

Babu sabani a tasakanin Malamai cewa yin tabligi a bayan liman ba tare da wata bukata ta Shari’ah ba bidi’ah ce a bar kyama.
Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya ce cikin Majmuu’ul Fataawaa 23/403 ((. : )). Ma’ana: ((Amma Tabligi bayan liman ba tare da wata bukata ba hakan bidi’ah ce ba mustahabbah ba a bisa ittifakin Shugabanni. Abin da aka sani Liman ne zai rika bayyanar da kabbara kamar yadda Annabi mai tsira da amincin Allah da Khalifofinsa suka kasance suna yi. Babu koda mutum guda da ya kasance yana yin tabligi a bayan Annabi mai tsira da amincin Allah, sai dai a lokacin da Annabi mai tsira da amincin Allah ya yi rashin lafiya sautinsa ya yi rauni Abubakar Allah Ya kara masa yarda ya kasance yana jiyar da kabbararsa. Hakika Malamai sun yi sabani game da cewa: Ko sallar mai yin tabligi tana baci? A bisa zantuka biyu cikin mazhabar Malik da Ahmad da wasunsu)).
Saboda abin da muka ji yanzu yana kyau al’ummarmu su sanya girmama sunnar Manzon Allah cikin dukkan ayyukansu na ibadah, su daure su daina yin tabligi a lokacin da mamu ke jin kabbarorin limaminsu, wannan ita ce Sunnah ta Annabi mai tsira da amincin Allah da babu sabani a cikinka adai gurin Malamai ba murakkaban jahilai ba.
Lalle muna sane da cewa wasu awaam su kan kafa hujja da cewa: Ai a Kasar Saudiyya ma ana yin tabligi, tunda kuwa haka babu ta yadda za a ce tabligi bidi’ah ce! A gaskiya irin wannan magana babu hujja a cikinta a dai gurin masu ilmin Musulunci; musamman ma ida aka san abubuwa kamar haka:-
1. Zatin ayyukan da za a gani ana yin su a kasar Saudiyyah ba ya zama hujjah ta Shari’ah, sai in su ayyukan sun dace da Shari’ah tukun, in har sun dace da Shari’ah to a lokacin ne za su zama hujja ba don zatinsu ba, a’a sai don dacewarsu da Shari’ah kawai.
2. Masallatai a kasar Saudiyya wadanda suke karkashin lurar hukuma ana kiyasta yawansu da dubbai ne, to amma babu inda ake yin tabligi sai a masallatai biyu kawai daga cikinsu; watau masallacin Haram na Makka, da masallacin Annabi mai tsira da amincin Allah na Madinah; su kuwa wadannan masallatai biyun ana yin tabligin ne a cikinsu ko dai saboda hukuma tana ganin girman da suke da shi da miliyoyin jama’a da ke salla a cikinsu a lokaci guda zai dace a ce a samu wani mai jiyar da muriyar liman saboda ta yiwu wasu mamun su kasa jin muryar liman saboda yawan mutane. In kuma wannan shi ne zai zama hujjar hukuma to kuwa lalle hujja ce mai matukar rauni; domin a dai halin da ake ciki na yin amfani da loudspeaker dukkan wani mai jin sautin Muballigi to kuwa lalle yana jin sautin shi kansa Liman din; wannan shi ne ya sa Malamai da dama suke cewa yin wannan tabligi na Haramaini sam badaidai ba ne. Ko kuwa muce ta yiwu ita hukuma tana nan tana kokarin kauda wannan bidi’ar ma ta tabligi kamar yadda ta yi kokari ta kauda wasu bidi’o’in da a da ake yin su a cikin haramin Makkah; watau kamar kauda bidi’ar yin salla daya tare limamai hudu na shahararrun mazhabobin da ake da su.
3. Koma dai mene dalilin da ya sa ake yin tabligi har yanzu a masallatai biyun nan kawai a kasar Saudiyya, wannan ba zai taba zama hujja ta Shari’ah ba wacce saboda ita ce za a bar Sunnah Tarkiyyah ta Annabi mai tsira da amincin Allah.
Allah muke roko har kullum da Ya dora mu a kan abin da yake shi ne daidai koda kuwa mafi yawan jama’a ba a kansa suke ba. Ameen.
Babu sabani a tasakanin Malamai cewa yin tabligi a bayan liman ba tare da wata bukata ta Shari’ah ba bidi’ah ce a bar kyama.
Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya ce cikin Majmuu’ul Fataawaa 23/403 ((. : )). Ma’ana: ((Amma Tabligi bayan liman ba tare da wata bukata ba hakan bidi’ah ce ba mustahabbah ba a bisa ittifakin Shugabanni. Abin da aka sani Liman ne zai rika bayyanar da kabbara kamar yadda Annabi mai tsira da amincin Allah da Khalifofinsa suka kasance suna yi. Babu koda mutum guda da ya kasance yana yin tabligi a bayan Annabi mai tsira da amincin Allah, sai dai a lokacin da Annabi mai tsira da amincin Allah ya yi rashin lafiya sautinsa ya yi rauni Abubakar Allah Ya kara masa yarda ya kasance yana jiyar da kabbararsa. Hakika Malamai sun yi sabani game da cewa: Ko sallar mai yin tabligi tana baci? A bisa zantuka biyu cikin mazhabar Malik da Ahmad da wasunsu)).
Saboda abin da muka ji yanzu yana kyau al’ummarmu su sanya girmama sunnar Manzon Allah cikin dukkan ayyukansu na ibadah, su daure su daina yin tabligi a lokacin da mamu ke jin kabbarorin limaminsu, wannan ita ce Sunnah ta Annabi mai tsira da amincin Allah da babu sabani a cikinka adai gurin Malamai ba murakkaban jahilai ba.
Lalle muna sane da cewa wasu awaam su kan kafa hujja da cewa: Ai a Kasar Saudiyya ma ana yin tabligi, tunda kuwa haka babu ta yadda za a ce tabligi bidi’ah ce! A gaskiya irin wannan magana babu hujja a cikinta a dai gurin masu ilmin Musulunci; musamman ma ida aka san abubuwa kamar haka:-
1. Zatin ayyukan da za a gani ana yin su a kasar Saudiyyah ba ya zama hujjah ta Shari’ah, sai in su ayyukan sun dace da Shari’ah tukun, in har sun dace da Shari’ah to a lokacin ne za su zama hujja ba don zatinsu ba, a’a sai don dacewarsu da Shari’ah kawai.2. Masallatai a kasar Saudiyya wadanda suke karkashin lurar hukuma ana kiyasta yawansu da dubbai ne, to amma babu inda ake yin tabligi sai a masallatai biyu kawai daga cikinsu; watau masallacin Haram na Makka, da masallacin Annabi mai tsira da amincin Allah na Madinah; su kuwa wadannan masallatai biyun ana yin tabligin ne a cikinsu ko dai saboda hukuma tana ganin girman da suke da shi da miliyoyin jama’a da ke salla a cikinsu a lokaci guda zai dace a ce a samu wani mai jiyar da muriyar liman saboda ta yiwu wasu mamun su kasa jin muryar liman saboda yawan mutane. In kuma wannan shi ne zai zama hujjar hukuma to kuwa lalle hujja ce mai matukar rauni; domin a dai halin da ake ciki na yin amfani da loudspeaker dukkan wani mai jin sautin Muballigi to kuwa lalle yana jin sautin shi kansa Liman din; wannan shi ne ya sa Malamai da dama suke cewa yin wannan tabligi na Haramaini sam ba daidai ba ne. Ko kuwa muce ta yiwu ita hukuma tana nan tana kokarin kauda wannan bidi’ar ma ta tabligi kamar yadda ta yi kokari ta kauda wasu bidi’o’in da a da ake yin su a cikin haramin Makkah; watau kamar kauda bidi’ar yin salla daya tare limamai hudu na shahararrun mazhabobin da ake da su.
3. Koma dai mene dalilin da ya sa ake yin tabligi har yanzu a masallatai biyun nan kawai a kasar Saudiyya, wannan ba zai taba zama hujja ta Shari’ah ba wacce saboda ita ce za a bar Sunnah Tarkiyyah ta Annabi mai tsira da amincin Allah.
Allah muke roko har kullum da Ya dora mu a kan abin da yake shi ne daidai koda kuwa mafi yawan jama’a ba a kansa suke ba. Ameen

YIN TABLIGI BAYAN LIMAN BA TARE DA BUKATA TA SHARI’A BA BIDI’A CE:YIN TABLIGI BAYAN LIMAN BA TARE DA BUKATA TA SHARI’A BA BIDI’A CE:

Aside