Fadakarwa/Tunatarwa, Taskar rubutukan malamai

Gaishe da mara lafiya – sheikh isa ali pantami

Sheikh Isa Ali
Pantami
ZUWA GAISUWAR
MARAR LAFIYA BABBAR
IBADA NE! Allah ya
mana karin LAFIYA da
IMANI,…
Imam Bukhari, Shaykhul
Islam da Ibn
Uthaymeen
(Rahimahumul Laah)
dukkansu sun tabbatar
da cewa zuwa gai da
majinyaci wajibi ne.
Amma Bn Uthaymeen
(RH) yana ganin cewa
yana halatta wani ya
wakilci wani a gaisuwa
ko kuma zuwan wasu
yasa wajibcin ya sauka
kan wasu “Fardhu
Kifaayah.”
Annabi (SAW) yana
cewa: ku ciyar da Mai Jin
Yunwa, ku ziyarci
MARAR LAFIYA, sannan
ku yanta Fursunoninku
(Bukhari).
FALALAR ZUWA
GAISUWAN: Annabi
(SAW) yana cewa: Duk
wanda yaje gaisuwa ga
marar lafiya da SAFE,
Mala’iku dubu saba’in
zasu masa Addu’ah har
zuwa yamma. Idan yaje
da Yamma Mala’iku
dubu saba’in zasu masa
Addu’ah har gari ya
Waye. Kuma ana masa
TANADIN LAMBU a
ALJANNAH. (Tirmithiy,
Sahihun ne a cikin Sahih
Tirmithiy).
Annabi (SAW) ya kara
da cewa: Lalle Musulmi
Idan ya ziyarci Marar
Lafiya to yana tafiya ne
a cikin inuwar Aljannah
har sai ya dawo.
(Muslim).
Yaa Allah ka bamu ikon
zuwa gaisuwa ga
marassa lafiya,…
June 2, 2013 at 2:56pm ·

Advertisements
Standard

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out / Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out / Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out / Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out / Change )

Connecting to %s