Fadakarwa/Tunatarwa, Taskar rubutukan malamai

ALAMOMIN KYAKYKYAWAN K’ARSHE! – sheikh isah ali pantami

Sheikh Isa Ali
Pantami
ALAMOMIN
KYAKYKYAWAN
K’ARSHE! Allah ya sa mu
cika da IMANI,..
Annabi (SAW) yana
cewa: Idan Allah yana
nufin BAWANSA da
ALHERI, sai yayi aiki da
shi. Sai aka tamabayi
Annabi (SAW) ta yaya
Allah zai yi aiki da shi?
Sai yace:Allah zai shiryar
da shi zuwa ga ayyuka
na kwarai gabannin
rasuwarsa (Imam
Ahmad, 11625; al-
Tirmidhi, 2142; saheeh
by Al-Albaani ya inganta
shi Saheehah, 1334).
ALAMOMIN CIKAWA DA
MUTUWAR SHAAHADA:
Akwai wasu alamomi
duk wanda ya rasu ya
samu dacewa da daya
daga cikinsu akwai
alamar ya samu
mutuwa mai nagarta,
kuma akwai alamun
yayi mutuwar
SHAHAADA.
1) RASUWA DA KALMAR
SHAHADA: Annabi
(SAW) yana cewa: Duk
wanda kalmar
karshensa ya zama
LA’ILA ILLA LAAH, zai
shiga ALJANNAH (Abu
Dawood, 3116; Saheeh
Abi Dawood, 2673).
2) RASUWA TA
HANYAR
MATSANANCIYAR
JINYA: Annabi (SAW)
yana cewa: MUMINI
yana rasuwa da JIBIN
GOSHI. (Ahmad, 22513;
Tirmidhi, 980; Nasaa’i,
1828).
3) RASUWA DALILIN
NAK’UDA ko RASUWA
DALILIN KOWACE CUTA
ALHALI MACE NA DA
JUNA: Annabi (SAW)
yace MATAR da ta rasu
tana da juna to tayi
SHAHADA. Duba (Abu
Dawood 3111).
4)RASUWA DALILIN
CUTAR ANNOBA: Duba
(Bukhaari, 2830; Muslim,
1916).
5) RASUWA RANAR
JUMU’AH KO DARENTA:
Duba hadisin Ahmad,
6546; al-Tirmidhi, 1074.
al-Albaani.
6) RASUWA A
TAFARKIN ALLAH: Duba
Al-Qur’an Suratu
Al-‘Imraan 3:169.
7) RASUWA DALILIN
CIWON CIKI: Duba
Sahihu Muslim, 1915.
8)RASUWA DALILIN
RUSHEWAR GINI KO
KUMA A RUWA: Duba
littafin Bukhaari, 2829;
Muslim, 1915.
9) RASUWA DALILIN
WUTA. Duba cikin
littafin Saheeh al-
Targheeb wa’l-
Tarheeb, 1396.
10)RASUWA DALILIN
KARE ADDINI KO
DUKIYA KO RAI: Duba
littafin Tirmidhi, 1421.
11) RASUWA A CIKIN
KYAKYKYAWAN AIKI:
Duba littafin Imam
Ahmad, 22813.
Yaa Allah ka mana
baiwa da kyakykyawan
karshe, sannan ka sa
mu yi MUTUWAR
SHAHADAH,…
By
Isa Ali Ibrahim Pantami

Advertisements
Standard

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out / Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out / Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out / Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out / Change )

Connecting to %s