Jibwis, SUNNAH

MALAMAI MASU TAFSIR TARE DA
ALARAMMOMI WADANDA KUNGIYAR
IZALA TA TURA ZUWA WASU
GARURUWA A CIKIN GIDA
NAIJERIYA, DOMIN GUDANAR DA
TAFSIRIN AZUMIN BANA NA
SHEKARAR 1438/2017. INSHA
ALLAH.
1. Sheikh Abdullahi Bala Lau da
Alaramma Nasiru salih Gwandu
Jimeta, Jihar Adamawa
2. Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo
da Alaramma Mato Gumau jos, Jihar
Plateau
3. Sheikh Dr. Ahmad Abubakar
Gumi da Alaramma Muhammad
Auwal
Sultan Bello, Jihar Kaduna
4. Sheikh Usman Isa Taliyawa da
Alaramma Abubakar Muh’d
Bolari, Jihar Gombe
5. Sheikh Ibrahim Sabi’u Jibiya da
Alaramma Aminu Salisu Jibiya
Jibiya, Jihar Katsina
6. Sheikh Yakubu Musa Hassan da
Alaramma Usman Birnin Kebbi
Katsina, Jihar Katsina
7. Sheikh Abbas Jega da Alaramma
Ridwan Kaduna,
Birnin Kebbi, Jihar Kebbi
8. Sheik h Dr. Abdullahi Saleh
Paskitan da Alaramma Abbas Iliyasu
Kano , Jihar Kano
9. Sheikh Muh’d Kabir Haruna
Gombe da Alaramma Ahmad
Sulaiman
T/Wada / Malali, Jihar Kaduna
10. Sheikh Abubakar Giro Argungu
da Alaramma khalilu mamba
Bargu, Jihar Niger
11. Sheikh Abdul Hadi da Alaramma
Yunusa Abubakar
Masallacin Danfodiyo, jihar Kaduna
12. Sheikh Usman Baban Tine,
Masallacin NNPC, Jihar
KadunaKaduna
13. Dr. Abdulmajid Umar
Rimi College, Kaduna
14 . Sheikh Habibu Yahya Kaura da
Alaramma Abubakar Adam
Sokoto, jihar Sokoto
15. Sheikh Dr. Ali Mustapha da
Alaramma Aminu Ibrahim
Ahmad, islamic center, Maiduguri,
Jihar Borno
16. Sheikh Aliyu Abdullahi Telex da
Alaramma Usman Barikin Ladi
Masj Haruna Danja, Jihar Kaduna
17 Sheikh Ahmad Muhammad Boyi
da Alaramma Mustapha Jalingo,
Masj bin Fodio, Jihar Taraba
18. Dr Ibrahim Abdullahi Sani Rijiyar
lemo da Alaramma yusuf suru
Area 11 Masjid, Abuja
19 . Mall. Aliyu Ladan da Alaramma
Nasiru Dan malam
Life Camp, Abuja
20 . Mal Hussaini Zakariya,
Bernex Plaza, Abuja
21. Mal. Abdullahi umar zaria da
Alaramma Salihu Gumi
Garki Village, Abuja
22. Mal. Auwal Mai Gaskiya da
Alaramma Aliyu Ibrahim Paki
Fed. Min. Abuja
23. Mal. Abdullahi Karshi
Villa, Abuja
24. Mal. Sahibul Kuwa
Dakkwa, Abuja
25. Dr Jamilu Muhammad Sadis da
Alaramma Idris Saminaka
AYA, Abuja
26 . Mal Abdulrahman Alzamfari da
Alaramma Saifullahi Kira
Berger Masjid, Abuja
27. Dr Ahmad Atiku Auwal
Gwarimpa masjidAbuja
28. Mal. Tajuddeen Imam da
Alaramma Murtala Muhammad
Prince & Princes, Abuja
29 . Mal. AbdulRahman Sani Yakubu
da Alaramma Sulaiman Abdullahi
Azare
Jiwa Emirate council, Abuja
30. Dr. Bashir Imam
Masjid Amb. Yola, Jihar Adamawa
32. Dr. Sadau Salihu
Yola, Adamawa
33. Dr. Abdulqadir Salih Kazaure
Jimeta, Jihar Adamawa
34. Mal. Ridwan Dahir Abubakar da
Alaramma Muhammad sani
malumfashi
Ganye, Jihar Adamawa
35. Mal. Mustapha Yusuf Hadeja,
Onitsha, jihar Anambra
36. Dr. Sani Umar Rijiyar Lemo da
Alaramma Abubakar Muh’d Rariya
Masjid Gwallaga, Jihar Bauchi
37 Mal. Alkali Sulaiman Yusuf da
Alaramma Dauda Muh’d Zukku
Masallachin Adamu Jumba, Jihar
Bauchi
38. Mal. Aliyu Sa’eed Gamawa da
Alaramma Sa’eed Adamu
Peoples Bank Masjid Gamawa, Jihar
Bauchi
39. Dr. Ibrahim Adam Umar Disina
da Alaramma Ukasha A. Umar
Masjid Rahama Jihar Bauchi
40. Mal. Adda’urrahman Alhassan
Sa’eed Adam, da Alaramma Nafiu A
A Sa’eed
Tilden Fulani, Jihar Bauchi
41. Mal. Muhammad Kabir Azare da
Alaramma Bala Bako
Azare, Jihar Bauchi
42. Dr. Zubairu Madaki da Alaramma
Kabir Abdullahi
Masjid Umar bn Al khattab, Kofar
Wambai, Jihar Bauchi
43. Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf
Guruntun da Alaramma Muhammad
Zahruddeen
Masj S19 Dutsen Tenshe jihar
Bauchi
44. Dr.Ismail kumo da Alaramma
Yusuf Dabai Mai 60
Makurdi, Jihar Benue
45. Mal. Aliyu Muhd Sani Adarawa da
Alaramma Isma’il maiduguri
Gboko, Jihar Benue
46. Mal. Ibrahim Albanin Kuri da
Alaramma Adam Mahmud
Kwayakusar, Jihar Borno
47. Mal. Dr. Muhammad Alh.
Abubakar da Alarama Baba Gana
Masjid Indimi Damboa RD,
Maiduguri, Jihar Borno
48. Sheikh Muhd Abubakar Kachalla
da Alaramma Ahmad Jiha Ismail
Maiduguri, Jihar Borno
49. Mal. Husani Yusuf Mabera da
Alaramma Mustapha Argungu
WarriJihar Delta
50 . Mal. Umar Jega da Alaramma
Iliyasu Birnin Gwari
Sapele, Jihar Delta
51. Mal. Nazifi Hashimu Samaru da
Alaramma Aliyu Ismaila Gummi
Benin City, Jihar Edo
52. Mal. Hassan Bako da Alaramma
Abdulhamid
Ado Ekiti, Jihar Ekiti
53. Mal. Adam Muhammad Adam da
Alaramma Abubakar Jibril Bula
Gombe jihar Gombe
54 . Dr Abdallah Umar Gadon Kaya
da Alaramma Baba Lawal Gombe
Kan bariki
(Water Board) Kumo, Jihar Gombe
55. Alaramma Nafiu Ismail Jigawa
Kazaure
56. Mal. Sulaiman Abubakar Birnin
Kudu
Yalwan Damai, Jihar Jigawa
57. Mall Isa Abdullahi da Alaramma
Hamza Isa Abdullahi
Hadeja, Jihar Jigawa
58. Mal. Sani Yakubu
Zaria, Jihar Kaduna
59. Mal. Muh’d Aminu Muhammad
da Alaramma Auwal Iliyasu
Saminaka, Jihar kaduna
60. Mal. Musa Asadus Sunnah
Kaduna, Jihar Kaduna
61. Mal. Murtala Nasir Almisry da
Alaramma Aliyu Dahir
ASD Motors, Jihar Kaduna
62. Mall Abdulrahman Maiduguri da
Alaramma Shamsuddeen Haruna
Rigachikun, Jihar Kaduna
63 . Mal. Sani Sulaiman Funtua da
Alaramma Baban gida Jalingo
Kafancan, Jihar Kaduna
64. Mal.Muhd Auwal Abubakar Mai
Shago da Alaramma Muhd Salis
Mu’az Almadani
Dar Hadith Magume Zaria, Jihar
Kaduna
65. Mall Shuaibu Salihu Zaria da
Alaramma Aliyu Umar
T/Wada zariaJihar kaduna
66. Mal. Muhammad Sani Alhamidy
Bebeji, Jihar kano
67. Mal. Abdul mudallib Ahmad
Tijjani da Alaramma Salihu Muhd
Usman
Masjid Triump, Jihar Kano
68. Mall Abdul mudallib Gusau
Alaramma Umar Ramadan
Kano State Univ. Wudil, Jihar kano
69. Mall Saifullahi Adam Shuaib da
Alaramma Tasiu Sabiu
Huguma Takai jihar Kano
70. Mall Husaini Yakubu Rano da
Alaramma Shamsuddeen Umar
Masjid Dar Tauheed Rano, Jihar
Kano
71. Mal. Aminu Usman (Abu Ammar)
da Alaramma Aliyu Usman Audi
Masjid Kerau, Jihar Katsina
72. Mal. Surajo Mahmud da
Alaramma Mukhtar surajo
Masjid Lowcost, Jihar Katsina
73. Mal. Nasir Abdurahman
Funtua, Jihar Katsina
74. Mal. Aminu Liman Mustapha
Masjid. Juma’a Funtuwa, Jihar
Katsina
75. Mal. Aminu Yammawa
Masjid. G.R.A.Jihar Katsina
76. Mal. Muktar Usman Jibiya da
Alaramma Auwal Umar
Matazu, Jihar Katsina
77. Mal. Musa Mansur da Alaramma
Salihu Ahmad
Masjid Karama Daura, Jihar katsina
78. Mal. Hassan Yusuf da Alaramma
Haruna Salisu
Masjid Senator (Madawaki) Daura,
Jihar Katsina
79 . Mal. Alkasim Umar Jibril Hotoro
da Alaramma Muhseen Ishaq
Aleiru, Jihar Kebbi
80 . Mal. Bello Bayawa da Alaramma
Muhammadu Bunza
Masj Shk Abubakar Mahmud Gumi,
Jihar Kebbi
81. Mal. Hashim Nata’ala Yawuri da
Alaramma Bala Abubakar Tambuwal
Dirin Daji, Jihar Kebbi
82. Mall Aliyu S Mafara da Alaramma
Usman Tagulle
Kamba, Jihar Kebbi
83. Mal. Usman Zaga da Alaramma
Adam Muhammad Fana
Bena, Jihar Kebbi
84. Mal. Ishaq M Alqali da Alaramma
Safiyanu Abdullai Makera
Danko Wasago, Jihar Kebbi
85 . Mal. Imam Aliyu Bunza da
Alaramma Amiru Ibrahim Argungun
Argungu, Jihar Kebbi
86. Mal. Umar Jega da Alaramma
Nafiu Bena
Koko, Jihar Kebbi
87 . Mal.Tasiu Funtuwa da
Alaramma Muhammad Bunza
Argungu, Jihar Kebbi
78. Mal. Imam Dahiru Lokoja da
Alaramma Ishaq
Lokoja, Jihar Kogi
89. Mal. Imam Yahaya Iddah da
Alaramma Auwal Muhammad
Iddah, Kogi
90. Mal. Yusuf Umar da Alaramma
Rabi’u Ibrahim
Obajana, Jihar Kogi
91. Mal. Salihu Muhammad da
Alaramma Ahmad Muhammad
Kaiama, Jihar kwara
92. Mal. Attahiru Kaiama da
Alaramma Ibrahim Kaima
Ilorin, Jihar Kwara
93 . Mall Mas’ud Ibrahim Offa
Offa, Jihar kwara
94 . Mal. Abubakar Abdulsalam da
Alaramma Tukur Jakada
Sabon masallaci Agege jigar Lagos
95 . Barrista Ishaq Adam
Jigar Lagos
96. Mall. Bukhari yakub da
Alaramma Muhammad fari
Agege LagosJihar Lagos
97. Mall Anas Assalafee Fagge da
Alaramma Abubakar Rano
Obalande/Ikoyi, Jihar Lagos
98 . Sheikh Imam Sulaiman
Masj 1000 & 4Jihar Layobe
99. Mal. Jamilu Albani Samaru da
Alaramma Abubakar Umar Balarabe
Lafia, jihar Nasarawa
100. Mall Adam Ibrahim Al-madani
da Alaramma Abbas Dahir Abubakar
Karu Masj Jibwis, Jihar Nasarawa
101 Mal. Shu’aibu Adam Makoli da
Alaramma Ibrahim Abubakar
Keffi, Jihar Nasarawa
102. Dr. Umar Gumi da Alaramma
Sulaiman Hussaini Doma
Doma, Jihar Nasarawa
103. Mal. Muh’d Sani Ahmad
(AbuRuqayya) da Alaramma
Abubakar Bawa
Wawa, Jihar Niger
104 Mal. Lawal Abubakar da
Alaramma Abdulrashid Jega
Minna, Jihar Niger
105 Mal. Mujittaba Yakubu Musa
Lafai, Jihar Niger
106. Mal. Abdulrahim Sabiu Rafin
Dadi da Alaramma Ibrahim yahuza
bauchi
Kontagora, Jihar Niger
107. Dr Umar GarbacDokaji da
Alaramma Muhammad Aliyu Kamba
Suleja, Jihar Niger
108 Mall. Muhammad Auwal Rijau
Mariga, Jihar Niger
109 Mall. Usman Arabi da Alaramma
Khalilu Bunza
RijauJihar Niger
110. Mall. Musa Mujaddadi
Lafai, jugwr Niger
111. Mal. Bukhari Ibn Ishaq Albayani
da Alaramma Yusuf Garba Jenuko
Shiroro, Jihar Niger
112. Dr. Abubakar Usman Pakistan
da Alaramma Ismail Abdullahi
Mangu
Yalwan Shendam, Jihar Plateau
113. Mal. Abubakar Musa Azi da
Alaramma Anas Abdullahi Y/
Shendam
Kanem, Jihar Plateau
114. Dr. Abdul-rahman Idris
Zakariya da Alaramma Ibrahim
Bukuru
Bukuru, Jihar Plateau
115. Mall Ibrahim Idris Zakariyya da
Alaramma Ibrahim Gangare
Masj Zinariya Jos, Jihar Plateau
116. Mal. Abdul-Azeez Dan-lami
(Dan Amar Kanam) da Alaramma
Saidu Yusuf Mr. Ali
Barkin Ladi, Jihar Plateau
117. Mall Isa Ibrahim Bawa Mai
Shinkafa da Alaramma Abdulkarim
Akwanga
Port-Harcourt, Jihar Rivers
118. Mal. Yunus Sa’eed Abdul-
Hamid
Refinery Depot, Jihar Rivers
119. Mal. Abdulbasir Isah Unguwar
Mai Kawo da Alarmma Muhd Bello
Argungu
Illela, Jihar Sokoto
120. Mal. Aliyu Aliyu Muhammad jos
da Alaramma Faruqu Jada
Tambuwal, Jihar Sokoto
121. Mal. Umar Mai Damma da
Alaramma Auwal Adam Sokoto
Masj sheikh Abubakar Gumi, Jihar
Sokoto
122. Mal. Abubakar Ladan Mai
Idigami da Alaramma Muhammad
Auwal Sokoto
Masj Lokoja Road jihar Sokoto
123. Mall. Sani Abubakar Tambuwal
Masjid Sultan Ibrahim Dasuki, jihar
Sokoto
124. Sheikh Dr. Mansur Ibrahim
Sokoto da Alaramma Abubakar
Ghani Sokoto
Masjid Abu Huraira, Jihar Sokoto
125. Mal. Muhammad Barkindo
Jungudo da Alaramma Abdullahi
Badejo
Masjid Ummah, Jihar sokoto
126. Mall Isa shehu Ruga
Masj Finance Jalingo, Jihar Taraba
127. Mal. Gambo Kyari Maiduguri da
Alaramma Mustapha Hamza Jarmai
WukariJihar Taraba
128 Mal. Khalid Usman Khalid da
Alaramma Salisu Ung. Kanawa
IbadanJihar Oyo
129. Mal. Yahaya Usman Gidadawa
da Alaramma Abubakar Kaura
ShagamuJihar Ogun
130. Mal. Khamis Nasidi da
Alaramma Idris Mararraba Abuja
AnkaJihar Zamfara
131. Mal. Surajo Muhammad Gusau
Gusau, Jihar Zamfara
132. Mal. Ishaq Kagara
dacAlaramma Garba Bayawa
Bukuyum, Jihar Zamfara
133. Mal. Aminu Numan da
Alaramma Hassan mall Sani
Tambuwal
GummiJihar Zamfara
134. Mal. Nuruddeen Numan da
Alaramma Bashir Gombe
Potiskum Jihar Yobe
135. Mal. Abdulaziz Muhd Bauchi da
Alaramma Sulaiman Funtuwa
Jaji MajiJihar yobe
136 Mal. Abubakar Salihu Dengi da
Alaramma Hashim Sani Hashim
GaidamJihar Yobe
137. Mal.Isa Aliyu Jen da Alaramma
Idris Gashuwa
GashuwaJihar Yobe
138 Mal.Ibrahim Damaturu da
Alaramma Sani Nguru
DamaturuJihar yobe
Mun samu Sanarwa Daga Kwamitin
Tafsiri Na kasa, tare da Sa Hannun
Shugaban kungiya ta kasa, Sheikh
Abdullahi Bala Lau.
Marubuci: Shugaban kwamitin
Jibwis Social Media ta kasa, Ibrahim
Baba Suleiman.
24/Sha’ban/1438. 21/May/2017.

Advertisements

MALAMAI MASU TAFSIR TARE DA ALARAMMOMI WADANDA KUNGIYAR IZALA TA TURA ZUWA WASU GARURUWA A CIKIN GIDA NAIJERIYA, DOMIN GUDANAR DA TAFSIRIN AZUMIN BANA NA SHEKARAR 1438/2017. INSHA ALLAH.

Aside
Abubakar Nuhu Koso, Siyasa, SUNNAH

Daga
Imam Murtadha Muhammad
Gusau
Lahadi, Maris 19, 2017
Bismillahir Rahmanir Rahim
Allah Ta’ala yace:
“Ya ku wadanda suka yi imani!
Ku kasance masu tsayuwa da
adalci, kuna masu shaida saboda
Allah, kuma ko da a kanku ne ko
iyayen ku da ‘yan uwanku
makusanta, ko ya kasance
mawadaci ko talaka, Allah ne
mafi cancanta da al’amarinsu,
kada ku bi son zuciya, har ku
karkata (ga rashin adalci). Kuma
idan kuka karkatar da magana
(saboda son zuciya), ko kuka kau
da kai (daga gaskiya), to, lallai
Allah ya kasance masani ga abin
da kuke aikatawa.” (Surah Nisa’,
4:135)
Kuma Allah Madaukaki yace:
“Ya ku wadanda suka yi imani!
Ku kasance masu tsayuwa domin
Allah, masu shaida da adalci.
Kuma kada kiyayya da wasu
mutane ta hana ku kuyi masu
adaci. Kuyi adalci. Shine mafi kusa
ga tsoron Allah. Kuma ku bi Allah
da takawa. Lallai Allah masani ne
ga abin da kuke
aikatawa.” (Surah Ma’idah, 5:8)
Allah ya jikan Mallam Sa’adu
Zungur yana cewa: “In zaka fadi,
fadi gaskiya, Ko me taka ja maka
ka biya!”
Ya ku ‘yan uwana masu girma!
Lallai wadannan ayoyin Alkur’ani
mai girma suna karantar da mu
umurnin Allah na yin adalci ga ko
wane mutum. Kar ka yarda
sabanin akida, ko sabanin addini,
ko sabanin yare ko harshe, ko
sabanin gari, jiha ko yanki, ko
sabanin launin fata, ko sabanin
siyasa, kai ko wane irin
banbance-banbance su hana ka
tsaida adalci ga wani mutum ko
wasu mutane. Duk yanda kuke
da sabani, yi kokari kaga cewa ka
yiwa kowa adalci. Yin hakan
shine za ya sa ka kubuta daga
afkawa cikin fushin Allah da
azabar sa.
Ya ku masoyan gaskiya da adalci!
Alal hakika Allah (SWT) ya
shar’anta muna yin nasiha, kuma
Annabi (SAW) ya ba ta
muhimmanci babba, har ya kai
ga fassara Addini da Nasiha,
saboda yadda nasihar take
daukar dukkan bangarori na
Addinin.
An karbo daga Tamim Bin Aus Al-
Dari, yace, Annabi (SAW) yace:
“ADDINI NASIHA NE.” SAI MUKA CE
GA WA? SAI YACE: “GA ALLAH, DA
LITTAFINSA, DA MANZONSA DA
SHUGABANNIN MUSULMAI, DA
GAMA GARINSU (TALAKAWA).”
Kuma Annabi (SAW) yace:
“WANDA YA GA MUMMUNAN ABU
DAGA CIKIN KU TO YA CANZA SHI
DA HANUN SA, IDAN BA ZAI IYA BA
TO YA CANZA SHI DA BAKIN SA,
IDAN BA ZAI IYA BA TO YA KI
ABUN A ZUCIYAR SA…”
Wadannan hadisai sun nuna
muna wajabcin yin nasiha ga
kowa da kowa, ko meye
matsayinsa, kai har da shugaba.
Kuma kalmar shugaba kalma ce
mai fadi, domin ta hada kowane
irin shugaba. Shugabannin
Addini ne, Shugabannin siyasa
ne, Shugabanni masu sarauta ne,
kai ko wadanne irin shugabanni.
Wajibi ne idan har an gano
kuskure a tattare dasu, ayi masu
nasiha.
Babu wani shugaba da aka ware
aka ce ban da shi a wurin yin
nasiha. Dole ne ayi ma shugaba
nasiha ko wanne irin matsayi
yake dashi a cikin al’ummah. A
Musulunci, babu wanda yafi
karfin doka, haka babu wanda
zai ce shi ya wadatu da nasiha ko
baya bukatar nasiha, matukar
alkhairi ne manufarsa. Kuma idan
shugaba ya karbi nasihar da
akayi masa, to zai amfana kuma
jama’ar da yake shugabanta su
amfana. Amma idan an yi masa
nasiha sai yayi fushi, kuma ya
dauki wanda yayi masa nasiha a
matsayin makiyi, saboda wasu
‘yan kanzagi da suka zuga shi, to
wannan shugaba zai cutu kuma
ya cutar da wadanda yake
shugaban ta.
Ya ku bayin Allah! Lallai duk
wanda yake bin abin da ke kai
kawo a sha’anin kasar nan tamu
mai albarka, Nigeria, yana sane
da labarin dake yawo a wurin
‘yan jaridu, kafafen yada labarai,
da sauran jama’a na wata wasika
da ta bulla satin da ya wuce, mai
take kamar haka: “IMMEDIATE
AND MEDIUM TERM IMPERATIVES
FOR PRESIDENT MUHAMMADU
BUHARI”, wasikar da take dauke
da shafuka talatin (30), wadda
Gwamnan Jahar Kaduna Mallam
Nasir Ahmad El-Rufa’i ya rubuta
wa Shugaba Muhammadu Buhari
yana mai bashi shawara da yi
masa nasiha a kan lallai ya gyara
sha’anin tafiyar da Mulkin sa,
kasancewar halin da ake ciki a
Nigeria da yanda ya hango
abubuwa suna gudana a cikin
gwamnati.
Ya ku jama’ah! Da farko, abunda
ya kamata ku fahimta shine,
wannan wasika ba fa a satin da
ya gabata aka rubuta ta ba, ko
watan da ya wuce, a’a. Wannan
wasika fa an rubuta ta ne tun
ranar September 22, 2016, wato
shekara daya da ta gabata, bayan
da farko gwamnan ya rubuta
wasu shawarwari da za su
taimaka wa shugaba Buhari
wajen gudanar da mulkin sa, a
shekarar 2015 bayan anci
nasarar zabe, kafin ya shiga
office. A cikin wasikar, Mallam
Nasir El-Rufa’i yake cewa: “A
matsayina na yaron ka, mai yi
maka da’a da biyayya, masoyinka
mai kaunar ka, mai fatan alkhairi
zuwa ga reka, mai son ci gaban
ka, ina fatan wannan nasiha za ta
taimaka. Amma idan ta bata
maka rai, ina rokon don Allah
kayi hakuri, ka yafe ni. Wajibi ne
in fada maka gaskiya, kuma ni
bani da wata manufa face ci
gaban jam’iyyar mu, ci gaban ka
a matsayin ka na shugaban kasar
mu, ci gaban gwamnatin mu da
ci gaban kasar mu.”
In dai fayyace maku, El-Rufa’i yayi
bayani dalla-dalla, cikakke na
inda ya hango matsaloli a cikin
gwamnatin Shugaba Buhari,
kuma yayi kira da a gyara domin
ci gaban kasar mu Nigeria.
A wannan wasika da ni na
karanta ta daga farko har
karshen ta, tsakani da Allah babu
inda Nasir El-Eufa’i ya soki Buhari
ko ya zage shi ko yaci mutuncin
sa. Kawai dai ya bashi
shawarwari ne game da sha’anin
kasa, da inda yake ganin akwai
kura-kuran da sune ummul
haba’isun da suke kawo tarnaki
wajen samar da canjin da aka
yiwa ‘yan Nigeria alkawarin
samarwa, da hanyoyin da za’a bi
domin magance su.
Bullar wannan wasika ke da
wuya, kawai sai wasu mutane da
suke ganin wai su masoya
Shugaba Buhari ne, Wadanda ba
gaskiya da adalci ne a gabansu
ba, suka yi caa a kan Gwamna El-
Rufa’i. Suka ce da wa aka hada
mu ba da shi ba? Mai zagi nayi,
mai batanci da cin mutunci nayi,
mai kage da karya da kazafi nayi.
Alhali wadannan mutane sun
manta, Shugaba Buharin da a da
can yasha alwashi kuma ya yanke
shawarar ba zai sake tsaya wa
takara ba, amma su El-Rufa’i suka
yi ruwa suka yi tsaki har suka
shawo kan sa ya amince ya tsaya
takara, kuma suka taimaka a
wurin kamfen matuka, takarar da
a wannan karon Allah yasa a kayi
nasara.
Wadannan mutane da suka yi caa
a kan El-Rufa’i, suna son su nuna
muna cewa Nasir El-Rafa’i baya
kaunar Shugaba Buhari, ko
Shugaba Buhari baya laifi, baya
kuskure ko duk abunda yayi dai-
dai ne, ko su kai shi matsayin
Allah, ko matsayin Annabta. Suna
son su nuna muna shi ma’asumi
ne, shiyasa suke yi masa irin
wannan makauniyar soyayyar da
za ta cutar da imanin su, tauhidin
su, akidar su da Musuluncin su.
Yanzu wadannan mutane suna
nufin sun fi El-Rufa’i son Shugaba
Buhari ne ko yaya? Suna nufin
Shugaba Buhari yafi karfin a
bashi shawara? Ko yafi karfin ayi
masa nasiha? Suna nufin su ce
muna soyayya ce da kauna ga
Shugaba Buhari irin wadda idan
yayi kuskure ayi shiru kar ayi
masa nasiha? Wadanne irin
mutane ne wadannan da suke
neman su halakar da shugaba da
sunan soyayya? Wallahi duk
Shugaban da ya rasa masu yi
masa nasiha da masu bashi
shawara ta gari, kuna ganin bai
yi hasara ba? Ta yaya Shugaba
zai ci nasara idan ba’a bashi
shawara kuma ba’a yi masa
nasiha?
Wasikar nan ma fa wasu miyagu
ne da basa kaunar zaman lafiya
da ci gaba suka kulla makircin
sakin ta a cikin jama’a don su
hada fitina da fada tsakanin
Shugaba Buhari da Gwamna El-
Rafa’i, ba don komai ba sai don
su cimma wata mummunar
manufa tasu ta son zuciya! Idan
ba haka ba, ta yaya wasikar da
aka yi tun wani lokaci, kuma
akayi ta a asirce, ace sai yanzu
kwatsam kawai wasu su bullo da
ita!
Ya ku ‘yan uwa! Wallahi ku sani
Shugaba​ Buhari mutum ne
kamar kowa. Yana yin dai-dai
yana yin kuskure. Inda yayi dai-
dai mu karfafe shi, muyi masa
Addu’a da fatan alkhairi. Inda
yayi kuskure kuwa, sai muyi
masa nasiha, mu bashi shawara
muyi masa Addu’ar Allah yasa ya
gyara.
Ba ma yiwa Shugaba Buhari
makauniyar soyayya ko
makauniyar biyayya. Ba mu
dauke shi marar laifi ko marar
kuskure ba. Dukkan Dan Adam
mai kuskure ne. Annabawan
Allah da Manzanni kadai ne
katangaggu daga zunubi, su
kadai ne ma’asumai. Amma duk
wanda basu ba, to ko waye shi
zai iya yin kukure.
Kuma mu sani, wallahi yiwa
shugabanni nasiha wajibi ne
kuma dole ne. Su kuma
shugabannin idan anyi masu
nasiha an basu shawara ta gari,
dole su dauka indai har da gaske
suke yi. Domin dukkan mu da su,
Allah zai tambaye mu.
Gwamna Nasir El-Rufa’i ba wai ya
rubuta wa Shugaba Buhari
wasika bane, ko ya bashi
shawara don neman wani
matsayi ba, kamar yadda wasu
shedanu suke fada. A’a, yayi
nasiha ne don a gyara. Kuma ya
sauke nauyin da ke kan sa har ga
Allah. Mu kuma Addu’ar mu har
kullun, shine, Allah ya ba Shugaba
Buhari ikon gyara wa, amin.
Ya ku Jama’a! Ba zai yiwu ba ace
duk lokacin da aka bai wa
Shugaba Buhari shawara ko aka
yi masa nasiha, kawai sai abu ya
zama bala’i. Wannan ya taba
faruwa har ma da mai dakin
Shugaban kasa, wato Hajiya
Aisha Buhari. Kawai don ta fadi
abun da ta hango zai kawo
matsala don a gyara, sai wasu
shedanu suka yi caa a kanta suna
zagi. Kuna nufin kun fi ta son
mijinta? Kun fi ta son cin nasarar
sa? Kawai don ta hango abunda
zai cutar da mulkin maigidanta
tayi magana sai abu ya zama
bala”i? Kar fa da sunan soyayya
mu kai wannan dattijo mu baro!
Wallahi ina ji muna tsoron mu
wuce gona da iri wajen soyayyar
wani, har a wayi gari mun wuce
ka’ida, ya zamanto muna yiwa
wani mutum irin soyayyar da ko
Allah da Manzonsa ba mu yiwa
ita! Don haka wallahi muyi
hankali, muji tsoron Allah a cikin
dukkanin al’amurran mu!
Dukkan wani mutum da yake mai
son ci gaba, mai kaunar Shugaba
Buhari da gaske, adili, kuma yake
kaunar adalci, wallahi dole ya
yaba wa Gwamna Nasir El-Rufa’i
a kan wannan jarunta tasa ta
yiwa Shugaban kasa nasiha. Da
yaso da sai ya zama dan amshin
shata, ya zama ba yada aiki sai
yiwa Shugaban kasa fadanci da
banbadanci, kamar yadda wasu
suka zabi yin hakan.
Sannan daga karshe, ina kira ga
Shugaba Buhari da yaji tsoron
Allah, na san zai ga wannan sako
nawa, kar ya dauki Nasir El-Rufa’i
a matsayin makiyinsa, wallahi
babban masoyinsa ne, mai
kaunar sa da gaske. Domin
mutum ba ya da masoyin da ya
kai ga wanda zai fada masa
gaskiya. Duk wanda zai zo gaban
Shugaban kasa yana fadanci, yaki
gaya masa gaskiya, wallahi ba
masoyinsa ba ne, munafuki ne.
Allah ya taimaki shugabannin mu
baki daya, ya hada kawunan su,
amin.
Wassalamu Alaikum,
Dan uwanku:
Imam Murtadha Muhammad
Gusau, daga Okene Jahar Kogi,
Nigeria. Za’a iya samun sa a
wannan number:
+2348038289761.

WASIKAR MALLAM NASIR EL-RUFA’I (MEMO) ZUWA GA SHUGABA BUHARI A MAHANGAR ADALCI

Aside
KYAKKYAWAN ZANCE

***KYAKKYAWAN ZANCE 010***
.
Aikin masu da’awah har kullum shi ne su gaya wa al’ummar Musulmi gaskiya a duk inda take; saboda a gudu tare a kuma tsira tare har zuwa gidan Aljannah, kuma tabbas duk wanda zaiyi da’awa dole ya gamu da matsaloli ta indama baya tsammani saboda haka dan uwa mai da’awa kawai kane mi yardan Allah, domin baza ka samu mutane su karbeta kamar yadda suke karban kudaden da suke samu bayan sunyi aiki ba, duba Tarihin Da’awar Annabin Allah Sallallahu Alayhi Wasallam yafi kowa gaskiya da tauhidi da hankali amma akace masa Mahaukaci, Masihirci, Makaryaci kai harma jifansa akayi a da’ib, amma bayan yayi hakuri yau gashi addinin yashi ko’ina a duniya.
Allah Muna Rokon Ka Yarda Damu, Ka Karbi Ayyukanmu.
.
Abubakar Nuhu Yahya
# IbnNuhAssunnee
04/05/1438
01/012/2017

***KYAKKYAWAN ZANCE 010***

Aside
KYAKKYAWAN ZANCE

***KYAKKYAWAN ZANCE 010***
.
Aikin masu da’awah har kullum shi ne su gaya wa al’ummar Musulmi gaskiya a duk inda take; saboda a gudu tare a kuma tsira tare har zuwa gidan Aljannah, kuma tabbas duk wanda zaiyi da’awa dole ya gamu da matsaloli ta indama baya tsammani saboda haka dan uwa mai da’awa kawai kane mi yardan Allah, domin baza ka samu mutane su karbeta kamar yadda suke karban kudaden da suke samu bayan sunyi aiki ba, duba Tarihin Da’awar Annabin Allah Sallallahu Alayhi Wasallam yafi kowa gaskiya da tauhidi da hankali amma akace masa Mahaukaci, Masihirci, Makaryaci kai harma jifansa akayi a da’ib, amma bayan yayi hakuri yau gashi addinin yashi ko’ina a duniya.
Allah Muna Rokon Ka Yarda Damu, Ka Karbi Ayyukanmu.
.
Abubakar Nuhu Yahya
# IbnNuhAssunnee
04/05/1438
01/012/2017

***KYAKKYAWAN ZANCE 010***

Aside
KYAKKYAWAN ZANCE

***KYAKKYAWAN ZANCE 009***
.
ME KAKE AIKATAWA YANZU?
KO KASAN MUTUWA ZATA IYA ZUWA MAKA A WANNAN LOKACIN?
FIYAYYEN HALITTA TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU KARA TABBATA AGARE SHI YACE; ZA’A TASHI KO WANNE BAWA (MUTUM DA AL’JAN) AKAN ABINDA YA MUTU AKANSHI.
YA DAN UWA KADA KAMANTA DA MUTUWA A KOWANEN LOKACI DA KAKE AIKATA AIKIN ALKHAIRI KO SHARRI.
ALLAH YA KARBI RAYUWARMU MANA MASU AIKATA ALKHAIRI.
.
Abubakar Nuhu Yahya
# IbnNuhAssunnee
04/05/1438
01/012/2017

***KYAKKYAWAN ZANCE 009***

Aside
KYAKKYAWAN ZANCE

***KYAKKYAWAN ZANCE 007***
.
Allah Subhanahu Wata’ala ya umarcemu da sadarda
zumunci zuwa ga “yan
uwanmu makusanta kamar
kanni ko yayyin mahaifi
da mahaifiya, “yan
uwanka na jini, dangika da
sauran abokan arziki.
ALLAH SUBHANAHU WA
TA’ALA YACE:- Ku baiwa
makusanta hakkinsu da
miskinai da matafiyi, kada
kuyi almubazzaranci,
Almubazzaranci.
{Suratul isra’i}
MANZON ALLAH SAW
YACE:- Wanda duk ya
kasance yayi imani da
Allah SWA da ranar karshe,
yasadar da zumuncinsa.
{Muslim}.
ALLAH YA BAMU IKON SADAR DA ZUMUNCI.
.
Abubakar Nuhu Yahya
# IbnNuhAssunnee
04/05/1438
01/012/2017

***KYAKKYAWAN ZANCE 007***

Aside
KYAKKYAWAN ZANCE

***KYAKKYAWAN ZANCE 006***
.
Iyaye sunada babban haqqi akan ‘ya’yansu, Haka suma ‘ya’ya sunada nasu hakkin a wurin iyayensu, na daga cikin haqqin ‘ya’ya a wurin iyayensu,
-Zaba Masu Suna Mai kyau
-Koya Masa ilimin Addini ko sanya shi a wurin dazai samu ilimi.
-In yakai shekarun balaga yayi masa Aure.
ALLAH YASA MU RABU DA IYAYENMU LAFIYA.
.
Abubakar Nuhu Yahya
# IbnNuhAssunnee
04/05/1438
01/012/2017

***KYAKKYAWAN ZANCE 006***

Aside